Bacewar $2.04bn, N164bn: An Maka Kamfanin Mai Na Najeriya NNPCL Kara a Gaban Kotu

Bacewar $2.04bn, N164bn: An Maka Kamfanin Mai Na Najeriya NNPCL Kara a Gaban Kotu

  • Ƙungiyar SERAP ta shigar da ƙara kan kamfanin mai na Najeriya (NNPCL) ƙara a gaban kotu kan ɓacewar wasu makuɗan kuɗaɗen shiga na man fetur
  • Kuɗaɗen $2.04bn da N164bn an yi zargin sun ɓace a wani rahoto da babban mai binciken kuɗi na tarayya ya fitar na shekarar 2020
  • Ƙungiyar ta buƙaci kotu ta tilastawa kamfanin na NNPCL ya yi bayanin yadda kuɗaɗen suka yi waɗanda ake zargin an karkatar da su ne

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar SERAP ta shigar da ƙara kan kamfanin NNPCL saboda gaza bada bayanan kuɗin shiga na man fetur $2.04bn da N164bn da suka ɓace.

A cewar SERAP ta shigar da ƙarar ne bisa zargin da babban mai binciken kuɗi na tarayya ya fitar a rahoton binciken shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Lauya ya hango kuskuren hukumar EFCC, ya yi gargadi

An kai karar NNPCL a kotu
SERAP ta shigar da kara kan NNPCL a gaban kotu Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

A rahoton ya yi zargin cewa kamfanin NNPCL ya gaza sanya kuɗaɗen cikin asusun tarayya, inda ya ce ta yiwu an karkatar da kuɗaɗen ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shigar da ƙarar ne mai lamba FHC/ABJ/CS/549/2024 a ranar Juma'a a babbar kotun tarayya da ke Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

Meyasa aka shigar da NNPCL ƙara?

A cikin ƙarar SERAP ta buƙaci kotun da ta umurci tare da tilastawa NNPCL ya yi bayanin inda $2.04bn da N164bn na kuɗaɗen shiga na man fetur, kamar yadda yake a cikin rahoton babban mai binciken kuɗi, rahoton Channels tv ya tabbatar.

SERAP ta kuma buƙaci NNPCL da ya miƙa masu hannu a cikin zargin ga hukumomin ICPC da EFCC domin bincike da gurfanar da su.

Ta kuma buƙaci NNPCL ya tabbatar da kwato kuɗaɗen da suka ɓace domin mayar da su zuwa asusun tarayya.

Kara karanta wannan

Malam El-Rufai zai kara da Tinubu a zaben shugaban ƙasa a 2027? Gaskiya ta bayyana

Ba a sanya ranar da za a fara sauraron ƙarar ba.

SERAP ta kai ƙarar Akpabio

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta maka shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da wasu tsofaffin gwamnoni tara da ke a majalisar dattawa ta 10 ƙara a kotu.

Ƙungiyar ta shigar da ƙarar ne bisa zargin karɓar kuɗaɗen fansho, yayin da suke karɓar albashi a matsayin sanatoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel