Manyan Labarai A Yau
Simbi Wabote tsohon shugaban hukumar NCDMB ya zargi karamin ministan man fetur da yin cushe a kasafin kudin hukumar. Heineken Lokpobiri ya yi martani.
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya shawarci sojojin Najeriya da su kafa sansanin sojoji a dajin Sambisa da tsaunin Mandara a jihar Borno.
An yada wani rubutu a shafukan sada zumunta cewa gwamnatin tarayya za ta fara biyan albashin ma'aikatan jihohi da kananan hukumomi. An gano gaskiya.
Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Ondo kuma jigo a jam'iyyar APC ya ce jam'iyyar za ta yi rashin nasara a zaben gwamna idan ba ta soke zaben fidda gwani ba.
Ofishin yada labarai na tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya fito ya kalubalanci hukumar EFCC da ta nuna shaida cewa ta taba gayyatar tsohon gwamnan.
Wasu yan bindiga sun kai sabon farmaki a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna inda suka kashe mutane. Miyagun sun hallaka mutum uku tare da sace wasu takwas.
Shugaban hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta kwato N120bn daga hannun 'yan damgara.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar cafke wasu mutum biyu da ake zargi da yi wa 'yan bindiga safarar makamai a jihar. Ta kwato bindigu masu yswa.
Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta sakwe shigar da kara kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari