Yahaya Bello: Lauya Ya Hango Kuskuren Hukumar EFCC, Ya Yi Gargadi

Yahaya Bello: Lauya Ya Hango Kuskuren Hukumar EFCC, Ya Yi Gargadi

  • Deji Adeyanju ya hango kuskure a binciken da hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ke yi a kan Yahaya Bello
  • Lauyan ya nuna cewa yadda hukumar ta ƙwato N990m daga makarantar da Yahaya Bello ya sanya ƴaƴansa akwai kuskure a ciki
  • Ya bayyana cewa kamata ya yi hukumar ta fara samun umurnin kotu kafin ta ƙwato kuɗaɗen daga makarantar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Barista Deji Adeyanju, tsohon daraktan yaɗa labarai na jam’iyyar PDP, ya ce hukumar EFCC na iya rusa shari'ar Yahaya Bello.

A kwanakin baya ne hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja, da laifin almundahanar kuɗi sama da Naira biliyan 80.

Kara karanta wannan

Malam El-Rufai zai kara da Tinubu a zaben shugaban ƙasa a 2027? Gaskiya ta bayyana

EFCC na binciken Yahaya Bello
Deji Adeyanju ya hango kuskure a binciken da EFCC ke yi wa Yahaya Bello Hoto: @OfficialGYBKogi, @OfficialEFCC
Asali: Twitter

Sai dai, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawan ba ta samu damar gurfanar da shi ba saboda rashin zuwansa kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yahaya Bello ya ƙi amincewa da yunƙurin cafke shi da EFCC ta yi a ranar 17 ga watan Afrilu, lokacin da jami’an hukumar suka dira a gidansa da ke Abuja.

Me lauyan ya ce kan binciken?

Da yake mayar da martani game da wasan kwaikwayon, Adeyanju ya bayyana a shafinsa na X a ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu, cewa akwai kuskure a ayyukan EFCC.

Lauyan ya ce Dala 760,000 (kimanin Naira miliyan 992) da EFCC ta ƙwato daga makarantar American International School of Abuja (AISA) "ba a bi hanyar da ta kamata ba".

A cewar ɗan gwagwarmayar, kamata ya yi hukumar EFCC ta fara samun umurnin kotu.

"Hukumar EFCC ba ta shirya ba, za ta iya rusa shari’ar Yahaya Bello, shari’a a kafar yaɗa labarai ba ta kamata ba. Kawai su kama mutumin, a tsare shi, a gurfanar da shi a gaban kuliya."

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Sanatan PDP ta yabawa EFCC tare da shawartar tsohon gwamnan

"Hatta kuɗaɗen da aka kwato daga makarantar America International School ba a yi yadda ya kamata ba, ya kamata EFCC ta fara samun umurnin kotu."

Martanin Yahaya Bello

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya musanta zargin da hukumar EFCC ta yi na cewa ya biya kuɗin makarantar ƴaƴansa daga asusun jihar Kogi.

Gwamnan ta hannun sakataren yaɗa labaransa ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a cikin zargin na EFCC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel