Dalilin da Ya Sanya Za a Iya Siyan Litar Man Fetur N570-580 a Watan Yuni

Dalilin da Ya Sanya Za a Iya Siyan Litar Man Fetur N570-580 a Watan Yuni

  • An yi hasashen farashin man fetur zai kasance tsakanin N570-580 a tsakiyar shekarar 2024 saboda dalilai biyu
  • A cewar Barista Titilope Anifowoshe, farfaɗowar da darajar Naira ke yi a kan Dala na iya yin tasiri wajen rage farashin man fetur
  • Titilope ta ƙara da cewa fara aikin matatar man Dangote shi ma zai yi tasiri sosai kan farashin man fetur a Najeriya nan gaba kaɗan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

An bayyanawa ƴan Najeriya yiwuwar siyan man fetur tsakanin N570 zuwa 580 nan da tsakiyar shekarar 2024.

Hakan zai auku ne bisa la’akari da ƙaruwar darajar Naira idan aka kwatanta da Dala a kasuwannin hada-hadar kuɗi.

Farashin man fetur zai sauka
An yi hasashen raguwar farashin man fetur Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Titilope Anifowoshe, ƙwararriyar lauya kuma ƴar kasuwa ce ta yi hasashen hakan a wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da ita.

Kara karanta wannan

Bayan matatar man Dangote, wani kamfanin mai ya rage farashin man dizal

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane tasiri matatar Dangote za ta yi?

Titilope ta kuma bayyana shigowar matatar man Dangote a harkar man fetur a matsayin babban abin da zai iya yin tasiri wajen rage farashin man fetur a kasuwannin Najeriya.

"Abubuwan da suka faru a baya-bayan nan game da dala da kuma shigowar Dangote cikin kasuwar mai na iya yin tasiri ga farashin man fetur (PMS) a Najeriya."
Raguwar farashin man dizal wanda ake amfani da shi wajen jigilar man fetur a motoci, zai taimaka wajen rage kuɗin da ake kashewa wajen jigilar man fetur wanda hakan zai sanya farashinsa ya sauka.
"Tare da zuwan matatar man Dangote, za a rage dogaro kan shigo da man fetur daga ƙasashen waje, wanda hakan zai ƙara rage kuɗaɗen da ake kashewa wajen jigilarsa."
"Waɗannan dalilan tare da farfaɗowar darajar Naira a kasuwa, za su iya taka muhimmiyar rawa wajen rage farashin man fetur."

Kara karanta wannan

Najeriya na asarar N1.29tr duk shekara saboda satar danyen mai, Abbas Tajudeen

“Bisa ga hakan, za mu iya hasashen cewa za mu iya ganin raguwar farashin man fetur tsakanin N570 zuwa N580 kan kowace lita zuwa watan Yuni."
"Sai dai, yana da kyau a lura cewa abubuwa da yawa na taka rawa wajen farashin man fetur da suka haɗa da farashinsa a kasuwannin duniya, shirye-shiryen gwamnati, da yanayin kasuwa."

- Titilope Anifowoshe

An rage farashin man dizal

A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin mai na MRS Oil Plc ya zaftare farashin man dizal zuwa N1,051 a faɗin gidajen mai mallakinsa a faɗin Najeriya.

Kamfanin ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan rage farashin man dizal da matatar man fetur ta Dangote ta yi da kusan kaso 60% a cikin 100%.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng