Gwamnatin Katsina Ta Yi Alhinin Kisan Kwamandan Sojoji a Jihar, Ya Samu Yabo

Gwamnatin Katsina Ta Yi Alhinin Kisan Kwamandan Sojoji a Jihar, Ya Samu Yabo

  • An shiga jimami da alhini a jihar Katsina kan kisan da ƴan sandan suka yi wa wani kwamandan sojoji a jihar a wani harin kwanton ɓauna
  • Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana kisan nasa a matsayin babban rashi duba da irin gudunmawar da ya bada wajen yaƙi da ƴan bindiga
  • Mazauna yankin da sansanin da yake jagoranta yake, sun nuna alhininsu kan kisan da aka yi wa Manjo Mohammed

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina da mazauna jihar na alhinin kisan wani kwamandan sojoji, Manjo Mohammed, wanda wasu ƴan bindiga suka kashe a ranar Alhamis.

An yi wa kwamandan kwanton ɓauna ne a wani sansanin sojoji da ke Sabon Garin Dan’Ali, a ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe wani babban kwamandan rundunar sojoji a jihar Katsina

Gwamnatin Katsina ta yi jimamin kisan kwamandan sojoji
Gwamnatin Katsina ta bayyana kisan kwamandan a matsayin babban rashi Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

An kashe shi ne a kusa da ƙauyen Malali da ke ƙaramar hukumar Kankara lokacin da ya amsa kiran kai agajin gaggawa, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shi ne kwamandan sansanin sojoji na Sabon Garin Dan-Ali da ke kan titin Kankara/Dutsinma.

Me gwamnatin Katsina ta ce?

Jaridar Daily Trust ta ce kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Katsina, Dakta Nasir Babangida Mu’azu, ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga jihar bisa la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen yaƙi da ƴan bindiga.

Ya ce, ba da dadewa ba gwamnatin jihar ta bayar da kyautar kuɗi N2m ga jami’in saboda jajircewarsa wajen kakkaɓe wasu mayaƙan da ke sansanin wani ɗan bindiga mai suna Modi-Modi da suka addabi yankin Safana da kewaye.

"Saboda godiya da irin rawar da ya taka a wancan lokacin, gwamna ya ba shi kuɗi N2m, na kuma ƙara masa N200,000, domin yabawa da ƙoƙarinsa da ƙarfafa masa gwiwa ya ƙara himma."

Kara karanta wannan

Masu kantin da ya hana 'yan Najeriya sayayya sun amsa gayyatar hukumar FCCPC

"Muna da dangantaka mai ƙarfi da shi a matsayin gwamnati. Muna matuƙar alfahari da shi, da kuma alhinin rasuwarsa, amma kuma muna farin cikin samun wannan shahada."

- Dakta Nasir Babangida Muazu

Mutane sun yi jimami

Shi ma da yake jawabi, wani mazaunin Kankara wanda ya ci gajiyar bajintar marigayin, ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen soja wanda ya sadaukar da kai kan aikinsa.

A ƙauyen da sansaninsa yake, mazauna ƙauyen su ma suna jimamin rasuwarsa, inda suka ce marigayi Manjo Mohammed yana tashi tsaye idan akwai wata barazana a duk ƙananan hukumomin da ke maƙwabtaka da su.

An jami'an tsaro motoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta rarraba motocin yaki guda goma ga jami'an tsaro domin taimaka musu wajen dakile rashin tsaro.

Gwamna Dikko Ummaru Radda na jihar ne ya rarraba motocin, inda ya bayar da su ga yankunan da rashin tsaro ya yi ƙamari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel