Manyan Labarai A Yau
Isra'ila ta farmaki gidan talabijin mallakin gwamnatin Iran a Tehran yayin watsa shirye-shirye. Iran ta yi Allah wadai da tare da yin kira ga MDD ta dauki mataki.
Iran ta kai hari da makamai masu linzami kan Isra'ila, wanda ya kashe mutane takwas. Isra'ila ta gargadi mazauna Tehran da su fice daga garin, ta karya lagon Iran.
Cibiyar CPPE ta bayyana cewa za ta samu tagomashi ta fannin fitar da ɗanyen mai sakamakon yakin Isra'ila da Iran, amma ta ce akwai matslolin da za su biyo baya.
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bukaci mazauna birnin Tehran na kasar Iran da gaggauta ficewa yayin da ake ci gaba da kai hare-hare.
Tsohon hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Aliyu Audu, ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru don ganin an kawo karshen mulkinsa a zaben shekarar 2027.
Jam'iyyar APC a yankin Kaduna ta Arewa ta bayyana goyon bayanta ga tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027. Ta kuma goyi bayan Uba Sani.
An kama wani mutum mai suna Esmail Fekri da laifin yi wa kasar Isra'ila leken asiri a kasar Iran. Kotun Iran ta rataye shi bayan tabbatar da aikata laifin.
Ministan harkokin waje na kasar Jamus, ya bayyana cewa kasashen Faransa, Birtaniya da Jamus sun shirya zama kan teburij tattaunawa da kasar Iran.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi magana kan hare-haren ta'addanci da ake kai a jihar. Ya ce makiyaya dauke da makamai marasa shanu ke kai hare-haren.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari