'Yan Adawa Sun Jawo Abin Magana, Gwamna Bala Ya Yi Masu Shagube kan Zabe
- Bala Mohammed ya ce jam’iyyun adawa da suka kaurace wa zaben kananan hukumomi a Bauchi matsorata ne saboda tsoron faduwa
- Jam'iyyar APM ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 20 da aka fafata a zaben
- Hakazalika, jam’iyyar ta kuma lashe kujerun kansiloli 319 daga cikin 323 da aka fafata wajen neman lashe su a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana jam’iyyun adawa da suka kaurace wa zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar a ranar Litinin a matsayin matsorata, yana mai cewa sun ji tsoron shan kaye.
Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyar APM ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 20 da aka fafata a zaben ranar Litinin, 17 ga watan Agustan 2026, kamar yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi (BASIEC) ta bayyana.

Kara karanta wannan
Osun 2026: Jerin manyan yan takarar gwamna 14, jam'iyyu, shekaru da matakin karatunsu

Source: Twitter
Hukumar ta kuma sanar da cewa ’yan takarar APM sun lashe kujerun kansiloli 319 daga cikin kujeru 323 da aka fafata a fadin jihar, cewar rahoton Tashar Channels tv.
Shugabar BASIEC, Jummai Abubakar, ce ta sanar da sakamakon bayan kammala kada kuri’a, kirga kuri’u, tattara sakamako da tantance su.
Gwamna Bala ya soki jam’iyyun adawa
Da yake magana bayan ya kada kuri’arsa tare da matarsa, Aisha, a rumfar zabensa da ke Dan Kungibar, ofishin Dagacin Bakin Dutse, Yalwan Duguri, a karamar hukumar Alkaleri ta jihar, gwamnan ya ce ya kamata jam’iyyun adawa su shiga zaben domin gwada karbuwarsu a tsakanin jama’a maimakon kaurace masa.
“Ina ganin wasu mutane matsorata ne. Har sun janye daga zaben saboda sun san za su fadi."
“Ba su yi yakin neman zabe ba. Da sun saurari shawarata, da sun shiga zaben domin su gwada karbuwarsu.” Inji shi.
Bala Mohammed ya ce zaben dama ce ga jam’iyyun siyasa su nuna irin karbuwarsu a wajen jama’a gabanin babban zaben 2027, yana mai jaddada cewa babu wata jam’iyya da za ta iya samun mulki a tsarin dimokuradiyya ba tare da goyon bayan masu kada kuri’a ba.
Gwamna Bala ya jinjina kan zaman lafiya
Ya kara da cewa yanayin zaman lafiya da aka samu a rumfunan zabe ya nuna cewa ana gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, jaridar The Punch ta kawo.labarin.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da shugabanci bisa tsarin dimokuradiyya da kuma bai wa jama’a damar amfani da hakkokinsu na kundin tsarin mulki.

Source: UGC
Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa zaben zai haifar da nasarar ’yan takarar da za su jagoranci kananan hukumomi cikin tsoron Allah.
Mohammed ya jaddada muhimmancin kananan hukumomi wajen ci gaban jihar, yana mai cewa mafi yawan harkokin da suka shafi rayuwar jama’a suna faruwa ne a matakin kasa da kasa, wato a matakin al’umma.
Shugaban masu rinjaye ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Bauchi, Saleh Hodi, ya yi murabus.
Saleh Hodi wanda ya kasance a majalisar tun shekarar 2019, ya yi murabus ne domin tsayawa takarar shugaban karamar hukumar Shira.
Asali: Legit.ng
