Tana tsaka da Musayar Wuta da Isra'ila, Ƙasar Iran Ta Yi Naɗi Mai Muhimmanci
- Iran ta naɗa Ali Madanizadehta a matsayin sabon ministan harkokin tattalin arziki da kudi domin shawo kan matsalolin da suka taso
- Wannan naɗi na zuwa ne a daidai lokacin da yaki ya ɓarke tsakanin Iran da Isra'ila, wanda ke ƙara ta'azzara
- Ali Madanizadeh ya zama sabon ministan tattalin arziki da kudi na Iran bayan ƴan Majalisa sun kaɗa masa kuri'ar amincewa yau Litinin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - 'Yan majalisar dokoki na Iran, a ranar Litinin sun amince da nadin sabon ministan tattalin arziki da harkonin kudi domin fuskantar matsalolin da ke ƙara ta'azzara.
Daga cikin kalubalen ake sa ran sabon ministan zai tunkara har da hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar kudin kasar Iran.

Asali: Twitter
Ali Madanizadeh, mai shekara 43, ya samu amincewar majalisar a matsayin sabon ministan tattalin arziki da kudi na kasar Iran yau Litinin, rahoton Tehran Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Iran ta naɗa ministan tattalin arziki
Wannan naɗi na zuwa ne watanni bayan an tsige, Abdolnaser Hemmati, ta hanyar kada kuri’ar rashin yarda saboda kasa shawo kan matsalolin tattalin arziki.
A cewar rahoton, Madanizadeh ya samu kuri’u 171 na goyon baya, 61 na adawa, sai kuma takwas da suka kauracewa kada kuri’a a cikin ’yan majalisar da suka halarci zaman.
Tattalin arzikin Iran na cikin matsin lamba tun bayan da Amurka ta ƙaƙaba mata takunkumi, wanda ya haddasa hauhawar farashi da kuma tsadar kayan masarufi.
Iran na fama da matsalolin tattalin arziki
Bayan komawar Shugaban Amurka Donald Trump ofis a watan Janairu, ya dawo da matakan “matsi mafi tsanani” kan Tehran ta hanyar takunkumi.
Wannan matsin tattalin arziki na faruwa ne a daidai lokacin da yaƙi ya ɓarke tsakanin Iran da Isra'ila.
Tun daga ranar Juma’a, Isra’ila ta fara kai hare-hare kan Iran, inda ta farmaki sansanonin soja, cibiyoyin nukiliya da kuma wuraren zaman jama’a.

Asali: Twitter
Musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila
Wadannan hare-hare sun hallaka akalla mutane 224 a ƙasar ta Musulunci, ciki har da manyan kwamandojin soja, masana nukiliya da fararen hula.
Iran ta mayar da martani ta hanyar harba jiragen yaki marasa matuki da makamai masu linzami, da suka kashe akalla mutane 24 a Isra’ila.
An daɗe ana tsama tsakanin ƙasashen biyu kuma tun tuni Iran ke zargin Isra'ila da kai mata hare-hare a ɓoye da nufin kashe masana kimmiyarta.
Wannan yaki da ke ƙara ta'azzara zai yi tasiri matuƙa kan tattalin arzikin Iran, wanda ake A ran sabon minista, Ali Madanizadeh zai yi koƙarin shawo kan lamarin.
Iran ta sake harba makamai zuwa Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa akalla mutane takwas suka mutu da Iran ta sake harba makamai masu linzami kasar Isra'ila yau Litinin.
Wadannan hare-haren na zuwa ne yayin da Isra'ila ta gargadi mutanen da ke zaune a tsakiyar Tehran da su gaggauta barin birnin.
Sojojin kasar Isra'ila sun fitar da irin wannan gargadi na bukatar kwashe fararen hula a sassan Gaza da Lebanon kafin kai hare-hare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng