An Zo Wajen: Gwamnan Benue Ya Fallasa Masu Hannu kan Kai Hare Hare a Jihar

An Zo Wajen: Gwamnan Benue Ya Fallasa Masu Hannu kan Kai Hare Hare a Jihar

  • Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya nuna yatsa ga makiyaya da ke ɗauke da makamai kan hare-haren da ake kai wa a wurare
  • Hyacinth Alia ya bayyana cewa makiyaya masu ɗauke da makamai da ke shigowa jihar ba tare da shanu ba, ke kai hare-haren
  • Gwamnan jihar ya nuna cewa wasu daga cikin masu kai hare-haren ma ba ƴan asalin Najeriya ba ne, suna shigowa ne daga waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana masu kai hare-haren ta'addanci a jihar.

Gwamna Hyacinth Alia ya bayyana cewa makiyaya ɗauke da makamai da ke shigowa jihar ba tare da shanunsu ba, su ne ke da alhakin kai hare-haren da suka auku a cikin ƴan kwanakin nan.

Gwamnan Benue ya magantu kan rashin tsaro
Gwamna Alia ya ce makiyaya ke kai hari a Benue Hoto: Rev. Hyacinth Iormem Alia
Asali: Facebook

Gwamna Hyacinth Alia ya bayyana hakan ne yayin da ake tattaunawa da shi a tashar talabijin ta Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe mutane a jihar Benue

A ranar Asabar, 14 ga watan Yuni, an kashe fiye da mutane 100 a hare-haren da ake zargin makiyaya da kai wa a ƙauyukan Yelewata da Daudu da ke ƙaramar hukumar Guma ta jihar Benue.

Rahotanni daga baya sun nuna cewa adadin waɗanda aka kashe ya haura 200 zuwa ranar Lahadi.

Me Gwamna Alia ya ce kan kashe-kashen Benue

A yayin hirar, Gwamna Alia ya bayyana cewa makiyayan na shigowa jihar ne ɗauke da bindigogi irin su AK-47 da AK-49.

Ya ce bayan makiyayan sun aikata kisan gilla da rushe ƙauyuka, wasu sababbin mutane na shigowa su mamaye wuraren da aka kai hari.

Gwamna Alia ya ƙara da cewa matsalar kan iyaka na daga cikin ƙalubalen da jihar ke fuskanta, domin galibin waɗanda ke kawo hare-haren na shigowa daga makwabciyar jihar ne wato Nasarawa.

Ya kuma ce wasu daga cikin masu kai harin na shigowa ne ta iyakar Kamaru, yana mai jaddada cewa ba duka ba ne ƴan Najeriya.

Gwamna Alia ya koka kan rashin tsaro a Benue
Gwamna Alia ya ce makiyaya ke da alhaki kan kai hare-hare a Benue Hoto: Rev. Hyacinth Iormem Alia
Asali: Facebook
"A bara, mutane sun koma ƙauyukansu suka fara noma, kuma sun samu amfanin gona sosai."
“Amma a bana, tun farkon lokacin fara noman, muka fara fuskantar wani sabon salo na hare-hare."
"Sabon salon na hare-haren da muke gani yanzu ya bambanta da rikicin manoma da makiyaya da muka sani a baya. Yanzu ya koma wani iri, inda makiyaya ke shigowa kuma masu ɗauke da makamai na cikinsu."
“Mun sanya musu suna ‘makiyaya ɗauke da makamai’. Abin da muke gani shi ne, ba shanu ake shigowa da su ba, sai dai waɗanda ke kan gaba wajen kai hare-haren su ne ke ɗauke da AK-47 da AK-49."
“Menene manufarsu? Ba sa zuwa da shanu ma. Su kan kai hari, su kashe mutane, kuma bayan mako ɗaya, wasu mutane su dawo su mamaye yankin."

- Gwamna Hyacinth Alia

JNI ta magantu kan kashe-kashe a Benue

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI), ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, ta yi magana kan kashe-kashen da aka yi a jihar Plateau.

Ƙungiyar ta nuna takaicinta kan hare-haren waɗanda suka jawo asarar rayukan mutane kusan 200 waɗanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

JNI ta bayyana cewa akwai baƙin ciki sosai kan yadda ake salwantar da rayukan fararen hula ba tare da sun yi laifin komai ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng