Bauchi: Ɗan Sarki kuma Hakimi Ya Rasu ba Zato ba Tsammani, Gwamna Bala Ya Yi Magana

Bauchi: Ɗan Sarki kuma Hakimi Ya Rasu ba Zato ba Tsammani, Gwamna Bala Ya Yi Magana

  • Iyan Jama'are kum Hakimin Hanafari, Alhaji Ahmed Nuhu Wabi ya rasu sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi ranar Lahadi
  • Gwamna Bala Mohammed ya yi jimami da alhinin wannan rashi, yana mai cewa rasuwar ta taɓa gaba ɗaya al'ummar jihar Bauchi
  • Ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin da masarautar Jama'are tare da addu'ar Allah SWT Ya jiƙansa kuma Ya gafarta masa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana jimami da alhini kan rasuwar Alhaji Ahmed Nuhu Wabi, Iyan Jama’are kuma Hakimin Hanafari.

Rahotanni sun nuna cewa basaraken ya rasu ne a wani mummunan haɗarin mota da ya rutsa da shi a ranar Lahadi a Bauchi da ke Arewa maso Gabas.

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.
Iyan Jama'are kuma.hakimin Hanifari, Alhaji Ahmed Nuhu Wabi ya rasu Hoto: Senator Bala Mohammed
Asali: Twitter

Gwamna Bala ya yi alhinin rasuwar hakimin Hanafari a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mukhtar Gidado ya fitar, kamar yadda Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bala ya yi alhinin rasuwar ɗan sarkin Jama'are

Bala Mohammed ya bayyana marigayi Ahmed Nuhu Wabi a matsayin basarake mai ƙima kuma ɗa ga mai martaba Sarkin Jama’are, Alhaji Nuhu Wabi.

Ya ce marigayin mutum ne mai sauƙin kai, da rikon amana, da kuma sadaukarwa ga al’ummarsa.

“A matsayinsa na Hakimin Hanafari, marigayin ya gudanar da aikinsa da ƙwazo da niyyar ciyar da al’ummarsa gaba, ta hanyar wanzar da zaman lafiya, adalci da ci gaba a yankinsa da ma wajensa,” in ji gwamnan.

Gwamna Bala ya miƙa sakon ta'aziyya

Gwamna Bala, a madadin gwamnati da al’ummar jihar Bauchi, ya miƙa ta’aziyyarsa ga masarautar Jama’are, iyalan marigayin da kuma dukan waɗanda lamarin ya shafa.

“Wannan babban rashi ne ba ga masarautar Jama’are kaɗai ba, har da dukan jihar Bauchi. Mun yi rashi na matashi mai albarka da kishin kasa wanda ajali ya riske shi ba tare da tsammani ba.

"Rasuwar hakimin wa'azi ne kan yadda rayuwa take da kuma ikon Allah SWT na karɓar ran kowane bawa cikin sauƙi."

- Bala Mohammed.

Gwamna Bala ya yi jimamin rasuwar Iyan Jama'are.
Gwamnati da al'ummar jihar Bauchi sun yi ta'aziyyar rasuwar Iyan Jama'are Hoto: Senator Bala Mohammed
Asali: Twitter

Sanata Bala ya yi addu'ar Allah jiƙan hakimin

Gwamnan ya kuma tabbatar wa da masarautar Jama’are cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba ta goyon baya tare da addu’o'i a wannan lokaci na bakin ciki.

A ƙarshe, Sanata Bala ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin, ya ji kan shi da rahamarsa, ya ba shi matsuguni a Aljannatul Firdaus.

Ya kuma roƙi Allah Ya ba iyalansa, mai martaba Sarkin Jama’are da dukan al’ummar masarautar haƙuri da juriyar wannan babban rashi.

Hatsarin mota ya yi ajalin ango a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa hatsarin mota ya yi ajalin wani ango, Garba Mustapha, a hanyar zuwa masallacin da za a ɗaura masa aure a jihar Bauchi.

An shirya ɗaura auren marigayin da amaryarsa, Khadija Adamu Sulaiman da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Asabar a babban masallacin Magama.

Wannan lamari ya girgiza ƴan uwa da abokan arziki, hatta mutanen yankin da angon, wanda ya kasance DPO na ƴan sanda, ke aiki sun kaɗu da samun labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262