Zaben 2027: Shugaba Tinubu Ya Sake Samun Tagomashi a Arewacin Najeriya
- Jam'iyyar APC a yankin Kaduna ta Arewa ta nuna amincewarta kan Shugaba Bola Tinubu ya yi tazarce a zaɓen 2027
- Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar sun kuma goyin bayan Gwamna Uba Sani da shugaban majalisar wakikai, Tajudeen Abbas ke sake neman wa'adi na biyu
- Sun nuna gamsuwa kan nasarorin da mutanen uku suka samu a lokacin da suka kwashe suna kan madafun iko
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Jam’iyyar APC a yankin Kaduna ta Arewa, wanda kuma aka fi sani da Zone 1, ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Jam'iyyar ta kuma goyi bayan gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, da shugaban majalisar wakilai ta ƙasa, Hon. Tajudeen Abbas, don su sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu.

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa an cimma wannan matsayar ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da aka gudanar a ɗakin taro na jami'ar ilmi ta tarayya da ke Zaria.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan APC sun goyi bayan Bola Tinubu
Taron ya haɗa manyan jiga-jigan jam’iyyar daga ciki da wajen gwamnati, ciki har da tsohon gwamna, ministoci masu ci da na baya, ƴan majalisar dokoki na ƙasa da na jiha, jakadu, kwamishinoni, shugabannin hukumomin gwamnati na tarayya da na jihohi, da shugabannin jam’iyya.
A yayin taron, jiga-jigan jam’iyyar sun bayyana muhimman nasarorin da gwamnatin APC mai mulki ta samu a matakin ƙasa da na jiha, ciki har da irin nasarorin da ShugabaTinubu, Gwamna Uba Sani, da Tajudeen Abbas suka samu.
An jaddada buƙatar ci gaba da zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya a jam'iyyar domin samun gagarumar nasara a zaɓen 2027.
Da yake jawabi kan muhimmancin haɗin kai gabanin zaɓen gaba, ministan muhalli, Malam Balarabe Lawal Abbas, ya ce, sai da haɗin kai da manufa ɗaya ne za a samu nasara mai ɗorewa ga jam’iyyar APC.
Shugaban majalisa ya yabawa Tinubu
A nasa jawabin, shugaban majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa fiye da Naira biliyan 50 an ware su cikin kasafin kuɗin tarayya na 2025 domin aiwatar da ayyuka a cikin ƙananan hukumomi takwas da ke cikin mazabar Arewacin jihar Kaduna.
Haka kuma ya bayyana cewa kusan makamancin wannan adadi an ware su domin manyan ayyuka a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria, jami’ar jihar Kaduna (KASU), da kwalejin ilmi da ke Gidan Waya.

Asali: Twitter
Shugaban majalisar ya gode wa Shugaba Tinubu da Gwamna Uba Sani bisa goyon bayan da suka bashi har ya kai matsayin shugaban majalisar wakilai, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Ya ce hanya mafi kyau ta nuna godiya da mayar da alherin da suka yi masa ita ce ta hanyar tashi tsaye wajen wayar da kan al’umma su fito su kaɗa ƙuri’a domin sake zaɓen shugabannin biyu.
Ya ƙara da cewa, nasarar su ce kadai za ta ba shi damar ci gaba da aikin alherin da yake yi.
Tinubu ya gana da wasu tsofaffin gwamnonin PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ga gana da wasu tsofaffin gwamnonin jam'iyyar PDP.
Shugaba Tinubu ya gana da gwamnonin ne a ƙarƙashin jagorancin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike.
Ganawar ta su ta zo a daidai lokacin da ake ta ƙoƙarin matsalar rikicin shugabanci da ya daɗe yana addabar jam'iyyar PDP
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng