Bayan Kulla Sulhu, Gwamnatin Katsina Ta Ja Kunnen Tubabbun 'Yan Bindiga

Bayan Kulla Sulhu, Gwamnatin Katsina Ta Ja Kunnen Tubabbun 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Katsina ta yi magana kan yarjejeniyar sulhu da aka ƙulla da wasu shugabannin ƴan bindiga
  • Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar ya gargaɗi tubabbun ƴan bindigan kan ka da su kuskura su sake komawa ruwa
  • Nasir Mu'azu ya bayyana cewa idan suka kuskura suka karya alƙawari, za a ci gaba da yi musu luguden wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta aika da saƙon gargaɗi ga ƴan bindigan da suka ajiye makamansu.

Gwamnatin ta gargaɗi tubabbun ƴan bindigan da su cika alƙawurran da suka ɗauka, ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

Gwamnatin Katsina ta ja kunnen 'yan bindiga
Gwamnatin Katsina ta gargadi tubabbun 'yan bindiga Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Nasir Mu’azu, ne ya yi wannan gargaɗin a ranar Litinin, 16 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ja kunnen tubabbbun ƴan bindiga

Nasir Mu'azu ya yi gargaɗin ne yayin da yake zantawa da manema labarai dangane da sababbin yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka ƙulla a jihar.

"Bari na bayyana cewa, idan har suka karya alƙawarin da suka ɗauka, to za mu dawo da yadda muke musu a baya. Wannan shi ne matsayar gwamnati."

- Nasir Mu'azu

Kwamishinan ya bayyana cewa wasu shugabannin ƴan bindiga daga ƙananan hukumomin Jibia, Batsari da DanMusa sun ajiye makamansu kuma sun amince su zauna cikin zaman lafiya da al’umma.

Ya tabbatar da cewa yankunan da abin ya shafa sun samu ci gaba wajen samun tsaro tun bayan da aka ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da su, rahoton Daily Post ya tabbatar.

“Gwamna Dikko Radda ya bayyana ƙarara cewa tsaro shi ne babban fifikonsa. Ayyukansa sun tabbatar da hakan. Ba za mu tattauna da ƴan bindiga ba, amma idan sun miƙa wuya, za mu ba su dama su rayu kamar sauran ƴan ƙasa."

- Nasir Mu’azu

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da kai hare-haren sojoji a wuraren da ke fama da rikici irin su Kankara, Faskari, Sabuwa, Dandume da Safana, sai dai idan ƴan bindigan da ke can suma sun ajiye makamansu.

"Idan har suka ci gaba da kai hare-hare, to za mu mayar da martani yadda ya kamata."

- Nasir Mu'azu

Gwamnatin Katsina ta ja kunnen 'yan bindiga
An gargadi tubabbun 'yan bindiga a Katsina Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Ƴan bindiga sun ajiye makamai

A ranar Asabar da ta gabata, shugabannin ƴan bindiga 10 daga DanMusa sun ajiye makamansu, ciki har da bindigogi ƙirar AK-47 da kuma bindigar PKT.

Haka kuma, sun sako wasu mutanen da suka yi garkuwa da su, ciki har da wata mata da ke ɗauke da cikin wata bakwai.

Kwamishinan ya ce gwamnati na maraba da zaman lafiya, amma ba za ta lamunci cin amanar yarjejeniya ba.

"Idan suka karya alkawurran da suka dauka, to za mu dawo da yadda muke mu’amala da su a baya."

- Nasir Muazu

Ƴan bindiga sun farmaki jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun farmaki jami'an tsaro a jihar Katsina.

Ƴan bindigan sun hallaka jami'ai biyar na rundunar tsaron jihar Katsina (C-Watch) a wani harin kwanton ɓauna da suka kai musu.

Miyagun ƴan bindigan sun kai musu harin ne a ƙauyen Maharba da ke ƙaramar hukumar Matazu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng