Labaran Duniya
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai da ba a san ko su wanene ba sun hallaka dan takarar shugaban kasa a kasar Mozambique. Sun kuma hallaka lauyan 'yan adawa.
Aliko Dangote wanda ya samu karayar arziki tun daga shekarar da ta gabata ya sake zama mafi arziki a Afirka. Arzikinsa ya karu da $15bn zuwa Oktobar 2025.
Majalisar dattawan Kenya ta kada kuri'ar tsige mataimakin shugaban kasar, Rigathi Gachagua kan cin hanci da rashawa da wasu tuhume tuhume 10 da ya musanta.
An harbi tsohon ministan jihar Maharashtra ba adadia kirji a wajen ofishin dansa a Mumbai wanda ya yi silar mutuwarsa, a cewar kafafen yada labarai na Indiya.
Wani matukin jirgin saman Turkiyya ya mutu bayan ya yanke jiki a cikin jirgin a lokacin da yake tuki, lamarin da ya sa jirgin ya yi saukar gaggawa a birnin New York.
A wannan rahoton za ku ji yadda kungiyar fafutuka ta Hezbollah ta bayyana cewa ana kara samun nasarori kan sojojin Isra’ila da ke kokarin kutsawa Lebanon.
Hukumar sadarwa ta NCC ta sanar da cewa za ta hukunta attajirin duniya Elon Musk bayan kamfaninsa na Starlink ya kara kudaden da yake caja ba tare da izini ba.
A Afirka, wasu daga cikin shugabannin kasashen nahiyar sun shafe shekaru da dama suna rike da madafun iko yayin da kuma suka haura shekaru 70 a duniya.
Rahotanni sun bayyana cewa Alkahira da ke kasar Masar ce babban birni mafi bunkasa a yawan jama'a a Afrika. Wannan kididdigar an sameta daga Majalisar Dinkin Duniya.
Labaran Duniya
Samu kari