Gaza: Tankokin Yakin Isra'ila Sun Bude Wuta kan Falasdinawa, an Kashe Mutane da Dama

Gaza: Tankokin Yakin Isra'ila Sun Bude Wuta kan Falasdinawa, an Kashe Mutane da Dama

  • Sojojin Isra'ila sun ci gaba da ta'addancin da suke yi a kan al'ummar Falasɗinawa da ke rayuwa a Zirin Gaza
  • Tankokin yaƙin Isra'ila sun yi ruwan wuta kan Falasɗinawan da suka taru domin karɓar kayan agaji da suka haɗa da abinci
  • Hakan ya jawo an samu asarar rayukan mutane da dama yayin da aka raunata wasu sama da kusan 200

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Zirin Gaza - Tankokin yaƙin Isra'ila sun buɗe wuta kan Falasɗinawa masu yawa a Zirin Gaza.

Buɗe wutar da tankokin suka yi ta jawo asarar rayukan Falasɗinawa 51 yayin da suke jiran motocin kayan agaji a Khan Younis da ke Kudancin Zirin Gaza.

Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa a Gaza
Tankokin Isra'ila sun bude wuta kan Falasdinawa a Gaza Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An tabbatar da rasuwar mutane a Gaza

Jaridar BBC ta rahoto cewa ma’aikatar lafiya ta Zirin Gaza ta tabbatar da rasuwar mutanen a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma’aikatar ta ƙara da cewa an jikkata ɗaruruwan mutane a lamarin.

Rahotanni sun ce a bayanan da likitoci suka bayar, fiye da mutane 200 ne suka jikkata, inda aƙalla 20 daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.

Me sojojinkasar Iara'ila suka ce?

Rundunar sojojin Isra’ila ba ta fitar da wani bayani kai tsaye game da wannan lamarin ba.

Shaidu sun bayyanawa jaridar Reuters cewa tankokin Isra’ila sun yi harbi kan dubban mutane da ke taruwa suna jiran kayan agaji.

Sashen jinya na asibitin Nasser ya cika maƙil da waɗanda suka ji rauni, lamarin da ya sa ma’aikatan lafiya suka kwantar da wasu a ƙasa da kuma a farfajiyar ɗakunan asibiti saboda ƙarancin wuri.

Wannan lamari na cikin jerin mummunan hare-hare da ke faruwa kusan kullum, inda Falasdinawa da dama ke rasa rayukansu yayin da suke neman taimako cikin ƴan makonnin da suka gabata.

Jami’an lafiyar yankin sun bayyana cewa aƙalla mutane 23 ne suka mutu sakamakon harbin Isra’ila a ranar Litinin yayin da suke kusantar wurin rabon kayan agaji na GHF a Rafah, da ke Kudancin Gaza.

GHF ta fitar da sanarwa a ranar Litinin tana cewa ta raba fiye da abinci miliyan uku a wurare huɗu ba tare da wata matsala ba.

Babu wata sanarwa kai tsaye daga rundunar sojin Isra’ila kan harbin da aka yi a ranar Litinin.

Isra'ila ta sake kashe Falasdinawa a Gaza
Isra'ila ta yi ruwan wuta kan Falasdinawa a Gaza Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Dakarun Isra'ila na kashe Falasɗinawa a Gaza

A lokuta da dama a baya, Isra’ila ta amince da cewa dakarunta sun buɗe wuta a kusa da wuraren ba da agaji, tana mai ɗora laifi kan mayaƙan Hamas da ta ce sune suke tayar da tarzoma.

Isra’ila ta dora nauyin rabon mafi yawan kayan agajin da ta amince su shiga Gaza a hannun GHF, wadda ke aiki a yankunan da sojojin Isra’ila ke ba da tsaro.

Majalisar ɗinkin duniya ta yi watsi da tsarin, tana cewa rabon kayan agaji ta hannun GHF bai wadatar ba, yana da hadari, kuma ya saɓawa ƙa’idojin ba da agajin jin ƙai.

Isra'ila ta kashe hafsun sojan Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin Isra'ila sun sanar da cewa sun hallaka wani babban soja a ƙasar Iran.

Sojojin sun bayyana cewa sun hallaka sabon babban hafsan sojojin Iran, Ali Shadmani a wani hari da suka kai a birnin Tehran.

Kisan Ali Shadmani na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Isra'ila da Iran ke ci gaba da musayar wuta a tsakaninsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng