Iran Ta Gano inda Isra'ila ke Hada Makaman Leken Asiri a Tehran

Iran Ta Gano inda Isra'ila ke Hada Makaman Leken Asiri a Tehran

  • Hukumomin Iran sun ce sun gano sansanin jiragen leƙen asirin Isra'ila a birnin Tehran da ake amfani da su wajen kai hare-hare
  • Wani rahoto da Legit ta samo ya bayyana cewa sansanin na Mossad yana cikin yankin Shahr-e Rey na birnin Tehran
  • Iran ta cafke mutane da dama da ake zargi da leƙen asiri yayin da take ci gaba da fallasa yadda Isra’ila ke shigowa cikin ƙasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Rahotanni daga Iran sun tabbatar da cewa jami’an leƙen asirin kasar sun gano wani katafaren sansanin Isra’ila da ake amfani da shi wajen harba jiragen leƙen asiri marasa matuƙa.

Wannan sansani da aka ce yana cikin yankin Shahr-e Rey da ke birnin Tehran, ana zargin shi ne ke ɗauke da kayan aiki na musamman da Mossad ke amfani da su wajen kai hare-hare.

Iran ta gano wajen hada makaman Isra'ila
Iran ta gano wajen hada makaman Isra'ila a Tehran. Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da kamfanin dillancin labaran Iran na Tasnim ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana cewa bayanai da bincike ne suka tona sirrin wannan wuri da ke cike da kayayyakin leƙen asiri.

Iran ta cafke mutane da ake zargi da leƙen asiri

A wani mataki na ƙara kare tsaron cikin gida, hukumomin Iran sun cafke mutane fiye da 80 da ake zargi da hannu a leƙen asiri ko goyon bayan Isra’ila.

A cewar rahoton CNN, mutum 28 daga cikin wadanda aka kama sun fito ne daga babban birnin kasar, inda aka zarge su da bai wa Isra'ila bayanan sirri.

A ranar Litinin, Iran ta aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani mutum da aka kama shekaru biyu da suka gabata bisa zargin leƙen asiri ga Isra'ila.

Ana ganin cewa wannan hukunci ya zama wani sako ga masu shirin yin haɗin gwiwa da abokan gaba.

Kasar Iran ta bukaci jama’a su rika kai rahoto

Ma’aikatar leƙen asirin Iran ta bukaci jama’a da su taimaka wajen gano masu haɗin baki da Isra’ila, musamman bayan an gano cewa Mossad na shigo da makamai cikin ƙasar.

Jami’an tsaro sun ce suna bibiyar wasu gidaje da ake zargin ana ajiyar makamai ko kuma ana gudanar da ayyukan da ba su dace ba a ciki.

Iran ta bukaci mka rahoton leken asiri
Iran ta bukaci mka rahoton leken asiri daga Isra'ila. Hoto: Getty Images
Asali: UGC

An fitar da wata sanarwa da ke ƙarfafa mutane su kai rahoton mutane masu sanye da hula da gilashi a cikin dare, ko kuma waɗanda ke karɓar manyan jakunkuna daga masu kawo kaya.

Kazalika, an bukaci a rika kula da sautin karar ƙarfe, hayaniya ko kururuwa daga cikin gidaje musamman waɗanda ke rufe tagoginsu ko da rana ne.

Iran ta kai hare-hare a kasar Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Iran ta harba makamai masu linzami fiye da 100 kasar Isra'ila a daren Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa Iran ta kai harin ne a matsayin ramakon gayya kan wani farmaki da Isra'ila ta kai mata.

Baya ga haka, Iran ta ce ba za ta taba yarda da tsagaita wuta ba matukar kasar Isra'ila na cigaba da kai mata hare hare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng