Kiwon Lafiya
Kasancewar Shinkafa ta zamto gama-gari a fadin duniya, domin kuwa abu ne mai wuya a rasata a gidan Talaka da mai kudi sakamakon yadda al'ummar duniya suka kafa mata kahon zuka na ta'ammali da ita kusan kowace rana zata hudo kai.
Kasancewar barasa akwai dadin dandano a baka da kuma harshe, hakan bai sanya ta tsarkaka da illata masu ta'ammalli da ita ba, ta yadda a wani sa'ilin take rugu-rugu da dukkan wata garkuwa ta lafiya da jikin dan Adam yake da ita.
Dan itacen Dabino baya da iyaka ta fuskar alfanu da kuma shahara a kasashen Larabawa, wanda ya samo asali tun a farkon duniya da ya kasance daya daga cikin nau'ikan abinci na Annabawa da mutanen da suka shude shekaru aru-aru.
Shi dai Kimchi wani nau'in abinci ne da ya fi shahara a al'adar mutanen kasar Koriya, wanda ake hada shi ta hanyar turara ganyeyyaki irin su Kabeji tare da kayan hadi domin kari dandano da suka shafi gishiri, tafarnuwa da citta.
Da yawan mutane sukan ribaci alfanun dake kushe cikin tafarnuwa wajen kiwatar lafiyar su. Akan yi amfani da ruwan tafarnuwa wajen kawar da cututtukan da suka shafi kirji inda take da matukar tasiri wajen kawar da cututtukan hunhu.
Masu bincike a bangaren kiwon lafiya sun gano maganin da zai rage karfin kwayar cutar kanjamau na tsawon watanni shida Binciken da masana kimiyya suka gudanar a taron samar da magungunan zamani karo na 25 a birnin Boston.
A yayin da cutar hawan jini ke neman zama ruwan dare mai gama duniya, akwai nau'ikan cututtuka biyar da kuma take haifarwa. Jaridar NAIJ.com ta kawo muku nau'ikan cututtuka biyar da hawan jini ke haifar wa kamar haka.
Wata kwararriya akan harkan kiwon lafiya, Helen Bulu, ta gargadi iyaye mata a Najeriya da su dain yi wa sabbin jarirai wanka da ruwan zafi da zarar an haife su da kuma al’adar fizgar hannu da kafafun su da ake yi da nufin yi musu.
Cutar Kanjamau tana daya daga cikin manyan cututtuka da suka addabi al'umma, sannan kuma daya daga cikin cutar da ta bawa masana wahala wurin samo maganin ta. Wannan shine jerin jadawalin kasashen da hukumar lafiya ta duniya ta...
Kiwon Lafiya
Samu kari