Bikin Sallah: Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wuraren shakatawa

Bikin Sallah: Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wuraren shakatawa

A yayin da musulmi a fadin duniya ke murna da farinciki raar sallar idi da kwanakin dake biye da ranar, gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da rufe wuraren shakatawa da wasan yara sabod dalilian tsaro.

Mai taimakawa gwamna El-Rufa’i na Kaduna a kan harkokin tsaro, Kanal Yusuf Yakubu, ya shaidawa BBC Hausa cewar sun dauki wannan hawara ne domin gujewa afkuwar fitina.

Kanal Yakubu ya kara da cewa wannan doka ba ta shafi hawan sallah da masarautusuka saba yi da salla ba tare da bayyana cewa hatta gwamna El-Rufa’I zai gudanar da hawan sallah a Kafanchan.

Bikin Sallah: Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wuraren shakatawa
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i

Garin Kaduna na daya daga cikin manyan biranen arewacin Najeriya da bikin sallah ke da matukar armashi. Yayin bukukuwan sallah, wuraren shakatawa da na wasannin yara kan cika makil domin nuna farinciki da kuma nuna nishadi na ganin irin wannan lokaci.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe malamin addini, sun sace matar sa a Kaduna

Sai dai a lokuta da dama a kan samu barkear rikiici tsakanin matasa ‘yan shara da aka fi sani da “’yan shara” a wuraren shakatawa dake garin Kaduna. Matasan kan yi amfani da lokutan bukukuwan domin aikata miyagun laifuka da suka hada da sata, kwace da ma satar mutane a wasu lokutan.

Wasu mazauna jihar ta Kaduna sun nuna gamsuwa tare da yabawa da wannan mataki da gwamnatin ta dauka tare da bayyana cewar hakan rage yawaitar asarar rayuka da ake samu lokacin bikin sallah duk da hanawar zata takura jama’a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel