An yankewa magidanci mai ‘ya’ya 7 hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kisan matarsa mai juna biyu

An yankewa magidanci mai ‘ya’ya 7 hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kisan matarsa mai juna biyu

Mai shari’a, Ntong Festus Ntong, na babbar kotun jihar Akwa Ibom dake zamanta a karamar hukumar Ikot Ekpene ta yanke hukunci a kan shari’ar wani magidanci da aka gurfanar bisa zarginsa da kisan matarsa mai dauke da juna biyu, shekaru hudu da suka wuce.

Kotun ta yankewa magidancin mai ‘ya’ya 7, Friday John Uko, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan gamsuwa da tuhumar da ake yi masa na zargin kisan matarsa Patience.

Alkali Ntong ya umar a rataye Mista Uko, dan asalin karamar hukumar Ikot Ossom ta jihar Akwa Ibom, har sai ya mutu, a matsayin hukuncin laifin day a aikta tun watan Agusta na shekarar 2014.

An yankewa magidanci mai ‘ya’ya 7 hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kisan matarsa mai juna biyu
An yankewa magidanci mai ‘ya’ya 7 hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kisan matarsa mai juna biyu
Asali: UGC

Kotun ta yarda cewar Mista Uko ya bugi matarsa da kafa a ciki, yayin da take dauke da juna biyu a karo na takwas bayan aurensu, lamarin day a jawo mata ballewar jini da ya zama silar mutuwar ta.

Tun farko, dan sanda mai gabatar da kara ya shaidawa kotun cewar takaddama ta barke tsakanin Uko da marigayiya Patience bayan ta dauki kudi, N1,000, a aljihun rigarsa domin dafa abincin da zasu ci a gidan.

DUBA WANNAN: Sunaye da laifuka: Hukumar 'yan sanda tayi babban kamun 'yan ta'adda da batagari a Katsina

Da yake yanke hukunci a jiya juma’a, Alkali Ntong, ya bayyana fushinsa yadda Mista Uko ya kasha matarsa mai juna biyu, da ya kamata yake lallabawa, a kan N1,000.

Alkali Ntong ya kara da cewa, “shari’ar ba wata mai sarkakiya ko daure kai ba ce tunda shi Mista Uko ya furta da bakinsa cewar shine ya jawo mutuwar matarsa saboda sabanin day a shiga tsakaninsu a kan N1,000.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel