Amfani 6 na shan Ruwan ɗumi ga Lafiyar 'Dan Adam

Amfani 6 na shan Ruwan ɗumi ga Lafiyar 'Dan Adam

A yau bankade-bankaden shafin jaridar Legit.ng ya leka faggen kiwon lafiya inda ya yaso muku wasu muhimman amfani da tasirin ta'ammali da ruwan ɗumi ga lafiyar 'Dan Adam, inda yake kawar da wasu kwayoyin cututtuka daban-daban.

Kamar yadda wata kwararriyar masaniyar kiwon lafiya kan ci da sha, Stella Metsova ta bayyana cewa ana bukatar kwankwadar ruwa ɗumi da sanyin safiya musamman tare da hadin lemun tsami domin dakile tasirin wasu kwayoyin halittu masu cutar wa da ake kira free radicals.

Amfani 6 na shan Ruwan ɗumi ga Lafiyar 'Dan Adam
Amfani 6 na shan Ruwan ɗumi ga Lafiyar 'Dan Adam

Binciken ya tabbatar da cewa, shan ruwan ɗumi ya kan tattare 'ya'yan hanji tare a inganta narkewa da tacewar abinci a cikin ciki.

Da sanadin shafin Life Hack, Legit.ng ta kawo muku jerin wasu muhimman amfani na kiwon lafiya da ruwan ɗumi ke yi ga lafiyar dan Adam.

1. Inganta narkewar abinci

Shan ruwan ɗumi da sfe kafin karin kumallo ya kan taimaka wajen inganta narkewar abinci da lafiyar 'ya'yan hanji.

2. Rage nauyi da maiko a jikin dan Adam

Ruwan ɗumi ya kan taimaka wajen rage nauyin jiki ta hanyar narkar da daskararren maiko da kuma teba.

KARANTA KUMA: Majalisar Wakilai ta bukaci Sufeto Janar ya lalubo makasan jami'an 'yan sanda 4 a jihar Edo

3. Hana tsufa da wuri

Bayyanar tsufa da wuri musamman ga mata wani kalubale ne da shan ruwan ɗumi da sanyin safiya kafin karin kumallo ya kan taimaka wajen rage saurin tsufa.

4. Saukaka ciwo

Musamman ciwon mara na mata yayin al'ada, shan ruwan ɗumi yana taka muhimmiyar rawar gani wajen rage ciwon jiki da ka iya bujurowa a koda wane lokaci.

5. Inganta gudanar jini

Shan ruwan ɗumi da sanyin safiya kafin karin kumallo ya kan taimaka kwarai da aniyya wajen kawar da wasu kwayoyin cututtuka na toxins domin inganta gudanar jini a jikin dan Adam.

6. Bacci mai annashuwa

Ko shakka babu kwankwadar ruwan ɗumi musamman kafin kwanciyar bacci bayan cin abincin dare ya kan agaza wajen tabbatar da samun kyakkyawan bacci mai dadin gaske.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng