Bayani kan Gilashin Meta da Baturiya ta Dauki Bidiyon Sarkin Daura da Shi

Bayani kan Gilashin Meta da Baturiya ta Dauki Bidiyon Sarkin Daura da Shi

  • Gilashin Meta wata na’ura ce ta zamani da ke ba mutum damar ɗaukar hotuna da bidiyo ba tare da riƙe waya ko kyamara a hannu ba
  • Na’urar tana ɗauke da ƙaramar kyamara, makirufo da lasifika, waɗanda ke ba mai amfani damar ɗaukar bidiyo, yin kira da sauraron kiɗa
  • Sai dai amfani da gilashin wajen ɗaukar hotunan mutane ba tare da izininsu ba ya haifar da muhawara kan kare sirrin jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gilashin Meta, wanda aka fi sani da Ray-Ban Meta Smart Glasses, na daga cikin sababbin na’urorin zamani da ke ba mutum damar ɗaukar hotuna da bidiyo ba tare da ya riƙe waya ko kyamara a hannu ba.

Kamfanin Meta ne ya ƙera na’urar tare da haɗin gwiwar kamfanin Ray-Ban, inda ya haɗa fasahar kyamara da wasu abubuwan amfani da ake samu a wayoyin zamani cikin gilashin ido.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi rugu rugu da tawagar APC ta yi hadari, an rasa rayuka da yawa

Gilashin meta
Gilashin meta da ake daukar bidiyo da shi. Hoto: Meta
Source: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa gilashin ya jawo hankalin jama'a da kuma muhawara kan yadda wasu za su iya amfani da shi wajen ɗaukar bidiyon mutane ba tare da sun sani ba.

Abubuwan da ke jikin gilashin Meta

Gilashin Meta ba kamar gilashin ido na yau da kullum ba ne, domin yana ɗauke da wasu na’urorin fasaha da ke ba mai amfani damar yin ayyuka daban-daban.

Ga wasu daga cikin abubuwan da ke jikinsa:

  • Ƙaramar kyamara
  • Ma’ajiyar bayanai
  • Lasifika
  • Makirufo

Haka kuma, wasu nau’ikan gilashin suna amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI), wadda ke ba mai amfani damar gudanar da wasu ayyuka ta hanyar magana da na’urar.

Yadda ake amfani da shi

Mai amfani da gilashin Meta na iya fara ɗaukar bidiyo ta hanyar danna maɓallin da ke jikinsa ko kuma ba da umarnin murya.

Abin da ya sa na’urar ta bambanta da kyamarar waya shi ne, mutum na iya ɗaukar bidiyo daga inda idanunsa ke kallo, ba tare da ya fito da waya ko wata kyamara ba.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da matar da ake zargin Sarkin Daura ya taɓa jikinta

Sai dai kamfanin ya sanya wata ƙaramar fitila a jikin gilashin, wadda ke haskakawa domin sanar da mutanen da ke kusa cewa ana ɗaukar hoto ko bidiyo.

Kamfanin Meta ya ƙaddamar da gilashin Ray-Ban Meta a shekarar 2023 tare da haɗin gwiwar kamfanin Ray-Ban.

Mark Zuckerberg da gilashin meta
Mai kamfanin Meta, Mark Zuckerberg. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Nawa ake sayar da gilashin?

A bayanan da aka gabatar a taron Meta Connect, sabon nau'in Oakley Meta Vanguard yana kan Dala 499, yayin da sabon Ray-Ban Meta ke kan Dala 379.

A Najeriya kuwa, farashin gilashin Ray-Ban Meta na iya farawa daga kusan Naira 300,000 zuwa Naira miliyan 3.5, gwargwadon nau'in gilashin da wurin da ake sayar da shi.

Daura: An nemi kare baturiya

A wani labarin, kun ji cewa Amnesty International ta yi Allah wadai da barazanar kisa da ake yi wa wata ’yar yawon buɗe ido ’yar Poland, Mirka Czee, bayan zargin cin zarafinta da ta yi wa Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk.

Kungiyar ta ce matar ta samu daruruwan sakonnin barazana, ciki har da gargadin cewa za a bi diddiginta domin kashe ta ko cutar da ita idan ba ta janye zargin da ta yi ba.

Amnesty International ta bukaci rundunar ’yan sandan Najeriya ta ba matar kariya tare da gudanar da bincike mai zaman kansa da adalci kan zargin cin zarafin da ta ce ya faru a fadar Sarkin Daura ranar 14 ga Nuwamba, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng