Aisha Buhari ta tafi 'Kasar Burkina Faso domin yawon wayar da kai kan yaki da Cutar Daji

Aisha Buhari ta tafi 'Kasar Burkina Faso domin yawon wayar da kai kan yaki da Cutar Daji

Wani rahoto da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bayyana cewa, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, ta fice daga birnin Abuja zuwa birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso domin halartar wani muhimmin taro.

Uwargidan ta shugaba Buhari za ta halarci wannan muhimmin taron da za a gudanar cikin kasar tta Burkina Faso domin wayar da kan al'umma dangane da yaki da cutar nan da ta Daji watau Kansa.

Aisha Buhari ta tafi 'Kasar Burkina Faso domin yawon wayar da kai kan yaki da Cutar Daji
Aisha Buhari ta tafi 'Kasar Burkina Faso domin yawon wayar da kai kan yaki da Cutar Daji

Uwargidan shugaban kasar Burkina Faso, Mrs Sika Kabore, ita ce mai masaukin baki da za ta daukin shirya wannan babban taro tare da hadin gwiwar kungiyar hadin kan musulunci ta OIC (Organisation of Islamic Coorperation) a cikin babban birnin kasar nan Ouagadougou.

Kakakin uwargidan shugaba Buhari, Mista Suleiman Haruna, shine ya bayar da wannan sanarwa yayin ganawa da manema labarai a fadar ta shugaban kasa.

KARANTA KUMA: Abubuwa 8 da baku sani ba game da tafiyar shugaba Buhari kasar Togo

Mista Suleiman yake cewa, wannan taro ci gaban wani babban taro ne da ya wakana a birnin Istanbul na kasar Turkey kan yaki da Cutar Daji a shekarar 2016 da ta gabata.

Kakakin ya ci gaba da cewa, za a gudanar da wannan gagarumin taro ne domin ilmantar da uwargidan kasashen biyu akan muhimmancin shugabancin wajen yakar da cutar Daji ta hanyar wayar da kan al'umma.

Haruna ya kara da cewa, tawagar uwargidan ta shugaba Buhari ta hadar da uwargidan gwamnan jihar Neja, Dakta Amina Bello da kuma Hajo Sani, babbar hadima ta musamman a wannan gwamnati.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng