Jihar Gombe na fama da barazana ta hadarin cutar Kuturta
Wani kwararren likitan Tarin fuka da kuma cutar kuturta, Dakta Mustapha Musa ya bayyana cewa, jihar Gombe na ci gaba da fama da barazanar ta hadarin cutar kuturta.
Dakta Musa ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Gombe a ranar Juma'a ta yau, inda yace binciken masana ya tabbatar da cewa cutar kuturta na ci gaba da yaduwa cikin birnin dake Arewacin kasar nan.
Kwararren likitan ya bayyana cewa, wannan matsala gami da barazana ta bayu ne sakamakon janye tallafi da cibiyar cutar kuturta ta kasar Holland ta yi cikin shekara guda da ta gabata.
A cewar sa, akwai cibiyar jakadancin kasar dake birnin Jos na jihar Filato, sai dai tun gabannin shekarar 2019 da ta gabata ya daina aiki da hakan ya janye duk wani tallafi ga cutar kuturta a kasar nan.
Ya ci gaba da cewa, wannan cibiyar na bayar da kulawa gami da tallafi ga jihohi 13 na kasar ya hadar har da jihar Gombe, inda a halin yanzu an samu kimanin mutane 13 da suka kamu da wanna cuta cikin watanni 20 da suka gabata.
KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta cafke masu satar kudi ta ATM a jihar Kano da Enugu
Sai dai ya yabawa kungiyar lafiya ta duniya watau WHO (World Health Organisation) dangane da azamar ta ta tunkarar lamarin a halin yanzu.
Legit.ng ta fahimci cewa, ana kamuwa da cutar kuturta ne ta hanyar wasu kwayoyin cututtuka da a turance ake ce masu Bacteria da kuma sunan su a kimiyance na mycobacterium leprae.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng