An Kashe Rayuka da aka Tarwatsa 'Yan Obi Kwankwaso a wajen Kamfen
- Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane shida tare da jikkatar wasu da dama a rikicin da ya barke yayin gangamin siyasa a jihar Delta.
- Lamarin ya faru ne a al'ummar Uduere da ke karamar hukumar Ughelli North, inda tawagar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ta ce wasu ’yan bindiga sun kai musu hari.
- Rundunar ’yan sanda ta ce an fara bincike domin gano hakikanin adadin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka haddasa rikicin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum shida da jikkatar wasu da dama a rikicin da ya barke yayin wani gangamin siyasa a jihar Delta.
An bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin a al'ummar Uduere da ke karamar hukumar Ughelli North ta jihar Delta.

Kara karanta wannan
Amurka ta kara sunayen 'yan Najeriya 24 cikin wasu 157 da za a fatattako daga kasar

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, CSP Ani Iniedu, ne ya bayyana adadin wadanda suka mutu a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Mutum 6 sun mutu a Delta
Iniedu ya ce rahoton farko da rundunar ta samu ya nuna cewa mutane shida ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
Ya kara da cewa rundunar ta lura da yadda adadin wadanda suka mutu ke bambanta a rahotannin da ake yadawa, don haka binciken da ake gudanarwa zai tabbatar da hakikanin adadin wadanda suka rasa rayukansu.
Kakakin rundunar ya ce Sufeto Janar na ’yan sanda, Olatunji Disu, ya umarci kwamishinan ’yan sanda na jihar Delta da ya gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa da zai dogara da hujjoji.
Ya ce binciken zai gano yadda lamarin ya faru, wadanda ke da hannu da kuma yadda jami’an ’yan sanda da aka tura wajen suka gudanar da aikinsu.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Mutane da dama sun mutu da aka yi yunkurin kashe sanata a wurin kamfe
Rundunar ta kuma yi gargadin cewa duk jami’in da aka samu da sakaci ko karya dokokin aikinsa zai fuskanci hukunci, yayin da za a gurfanar da duk wanda aka samu da aikata laifi a gaban kotu.
An sanya dokar hana fita
Rundunar ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar Delta ta sanya dokar hana fita daga magariba zuwa safiya a duk fadin karamar hukumar Ughelli North.
Dokar za ta kasance daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a kowace rana har sai gwamnati ta ba da wani umarni.
Iniedu ya ce rundunar ’yan sandan jihar na aiwatar da dokar, tare da kara yawan jami’an tsaro da sintiri domin hana sake barkewar rikici.

Source: Original
Ya bukaci mazauna yankin, shugabannin al'umma da ’yan siyasa su kwantar da hankalinsu, su bi dokar hana fita tare da kauce wa yada bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba.
'Yan APC sun rasu a Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa akalla magoya bayan jam’iyyar APC 15 sun mutu, yayin da wasu 27 suka jikkata bayan motar dakon kaya da ke dauke da su ta yi hatsari a jihar Zamfara.
Mutanen na kan hanyarsu ne daga kauyukan Falale, Dankosa da Iyaka da ke karamar hukumar Gummi zuwa Talata Mafara domin halartar gangamin kaddamar da yakin neman zaben Gwamna Dauda Lawal.
Wata majiya mai masaniya kan lamarin da wasu mazauna Gummi ta ce mutum 14 sun mutu a wurin da hatsarin ya faru, yayin da wasu uku suka rasu jim kadan bayan an yi sallar jana'izar wadanda suka mutu a wurin.
Asali: Legit.ng
