Da magani a gonar yaro: Amfani guda 7 da Fara ke yi ga jikin dan Adam
Cin Fara ba sabon abu bane a Najeriya, musamman a yankin Arewacin Najeriya, inda ko a garin Daura da Katsina ana siyar da Fara kwano kwano, kuma ga wadanda suke ci ko suka taba ci, sun tabbatar cewar yana dadi a baki, kuma yana da zaki.
Sai dai dama Hausawa na cewa da magani a gonar yaro, amma bai sani ba, wannan ya sanya Legit.ng kawo muku jerin amfanin cin fara ga jikin dan Adam, wanda aka gano bayan wani zuzzurfan bincike da masana daga jami’ar Wisconsin-Madison Nelson suka yi.
KU KARANTA: Zakaran gwajin dafi: Dalibi daga Arewacin Najeriya ya yi zarra a jarabawar JAMB
Wata mashahuriyar Malama a jami’ar, mai suna Valerie Stull ce ta jagoranci wannan bincike akan Fara, inda tace bincikensu ya nuna akwai mutane biliyan biyu a Duniya dake cin Fara, haka zalika daga cikin amfanin Fara akwai:
Samar da kwayar ‘Probotic’ dake da matukar amfani da jiki
Hana kumburin jiki
Karin jini a jikin dan Adam
Kara karfin garkuwan jiki
Kara karfin kasusuwan jikin dan Adam
Samar da kiste da dumama jikin dan Adam
Taimakawa wajen farfasa abinci a jikin dan Adam
Daga karshe Dakta Valerie ta ce a yanzu haka mutane suka na kara wayewa game da cin Fara, kuma masana sun karkata wajen bincike daban daban akan Fara don gano hanyoyin bunkasa amfaninsa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng