Kayan makaranta daga China na iya kawo cutar daji - SON

Kayan makaranta daga China na iya kawo cutar daji - SON

- Hukumar kula ta ingancin kayayaki na Najeriya (SON) tayi gargadi kan yadin tufafin makaranta mai janyo Cancer

- Binciken da akayi ya nuna cewa an samu sinadirin 4-amino azo dye a cikin kayan wasu manyan kamfanonin kera yadi na China

- Bincike ya nuna sinadarin da ke jikin tufafin na hadewa da zufa kuma yakan fitar da sinadarin da ka iya janyo cutar daji

Hukumar kula da ingancin kayayaki na kasa (SON) ta gargadi makarantu da ke sayo kayan makarantan dalibansu daga kamfanonin Sing Fat School Clothier Company da Zenith Uniform Company da ke kasar Sin da suyi hattara saboda an gano wani sinadari mai janyo cutar daji (Cancer) a cikin yadin da kamfanonin.

Kayan makaranta daga China wai yana iya kawo cutar daji - SON
Kayan makaranta daga China wai yana iya kawo cutar daji - SON
Asali: Twitter

Kakakin hukumar SON, Osita Aboloma, ya ce an gano sindarin 4-amino azo dye a cikin kayan makarantar daliban wasu makarantu da ke Hong Kong inda aka samu kimanin miligram 173 da miligram 41 a cikin yadin kuma wadandan adadin sun haura adadin da aka amince a rika amfani dashi.

KU KARANTA: 2019: Mataimakin Ali Modu ya ankarar da Buhari tuggun da tsohon maigidan nasa ke kulla masa

Ya ce tuni kasashen turai, Japan da sauran kasashe sun haramta amfani da 4-amino azo dye tun kafin ayi wannan binciken.

"Sinadarin na fitar da kwayoyin da ke iya janyo cutar daji muddin tufafin suka hadu da gumi ko zufa, hakan yasa kasashe da dama suka haramta amfani da su."

"Masu sayo kayan makaranta daga kasashen waje a Najeriya sai su tabbatar sun bi dokokin hukumar SON domin a tattance kayayakin da za su sayo a karkashin shirin SONCAP saboda gujewa shigo da irin wadandan abubuwan masu hadari cikin kasar."

Aboloma ya shawarci dukkan wadanda suka riga suka sayo kayan makaranta daga kasar China su garzaya zuwa dakin gwaje-gwaje na SON domin da ke Kaduna domin a tabbatar da cewa basu dauke da sinadarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel