Amfani 6 na Man Lemun tsami ga Lafiyar 'dan Adam

Amfani 6 na Man Lemun tsami ga Lafiyar 'dan Adam

A yau kurda-kurda da kalacen rahotanni da suka danganci kiwon lafiya na jaridar Legit.ng ya kawo ma ku wasu muhimman sirraka da man lemun tsami ya kunsa ga lafiyar dan Adam wajen inganta ta a sakamakon wasu sunadarai da ya kunsa.

Ko shakka ba bu kamar sauran 'ya'yan itatuwa akwai muhimman sirraka na kiwon lafiya da lemun tsami ya kunsa a sanadiyar yalwar arziki ta wasu sunadarai da ya kunsa masu yakar cututtuka gami da garkuwa da kuma bayar da kariya ga lafiyar dan Adam.

Amfani 6 na Man Lemun tsami ga Lafiyar 'dan Adam
Amfani 6 na Man Lemun tsami ga Lafiyar 'dan Adam
Asali: Depositphotos

Binciken masana kiwon lafiya ya tabbatar da cewa, ana amfani da sunadarai da lemun tsami ya kunsa wajen hada magunguna da dama da kuma kayan kwalliya na a sakamakon tasirinsa wajen gyara fatar jiki.

Masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, man lemun tsami ya kunshi sunadaran; limonine, terpene, linalool da kuma citral.

KARANTA KUMA: Inyamurai ke da'awar akidar Yarbawa ta sauya fasalin Najeriya - Yakasai

A yayin da hausawa kan ce lafiya jari ce ga dukkan mai ita, man lemun tsami yana taka rawar gani wajen kawar da jerin cututtuka da inganta lafiyar jiki da suka hadar da:

1. Magance ciwon jiki a gabbai

2. Ana kurkurar baki da man lemun tsami domin kawar da cutar wari da hamami na baki.

3. Man lemun tsami yana kara haske da kuma inganta karfin hakori.

4. Ciwon mura da mashako.

5. Man lemun tsami yana inganta lafiyar fata ta hanyar kawar da kurajen gona, cin zanzana, tattarewar fata da kuma disashewar tabo a fuska.

6. Sunadaran da man lemun tsami ya kunsa yana inganta lafiyar gasu musamman na ka ta hanyar kawar da amosani da kuma zubewar gashi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng