Ikon Allah: wata mata ta haifi jariri da ido daya a tsakiyar goshi, hotuna

Ikon Allah: wata mata ta haifi jariri da ido daya a tsakiyar goshi, hotuna

- Wata mata ta haifi jariri da ido guda daya tal a tsakiyar goshi a kauyen Kayu Jati dake yankin Panyabungan a kasar Indonesia

- Haihuwar yaron ta girgiza tare da jefa likitocin kasar Indonesia cikin nazari domin gano dalilin haihuwar jaririn cikin irin wannan yanayi

- Jaririn shine yaro na farko da ya zo da irin wannan matsala cikin yara 5 da Atana Ariyanto da uwargidansa, Suriyanti, suka haifa

Likitoci a kasar Indonesia sun matukar girgiza bayan wata mata ta haifi wani jariri mai ido daya a tsakiyar goshi da kofar hanci guda daya amma kuma da ragowar cikakkun halittu na dan adam.

Rahotanni sun bayyana cewar jaririn, shine yaro na biyar da iyayensa suka haifa. Sai dai wannan shine karo na farko da uban jaririn, Atana Ariyanto, da uwargidansa, Suriyanti, suka fuskanci irin wannan lamari mai matukar daure kai.

Ikon Allah: wata mata ta haifi jariri da ido daya a tsakiyar goshi, hotuna
Ikon Allah: wata mata ta haifi jariri da ido daya a tsakiyar goshi
Asali: Depositphotos

Ikon Allah: wata mata ta haifi jariri da ido daya a tsakiyar goshi, hotuna
Ikon Allah: wata mata ta haifi jariri da ido daya a tsakiyar goshi
Asali: Depositphotos

Mahifiyar jaririn, Suriyanti, ta haihu ne ba tare da fuskantar wata wahala ba a wani asibiti, Rumah Sakit Umum Daerah, ranar Alhamis.

DUBA WANNAN: Annoba: Mummunar ambaliyar ruwa ta kashe mutane 31, ta rushe gidaje fiye da 10,000 a Kano

Rahotanni sun bayyana cewar Suriyanti ba ta yi gwajin na’ura don sanin halin da jaririn dake cikinta ke ciki ba kafin haihuwa ba. Sai dai bayan ta kalli abinda ta haifa, ta ruga wani daki ta kulle kanta.

Ikon Allah: wata mata ta haifi jariri da ido daya a tsakiyar goshi, hotuna
Suriyat da jariri mai ido daya da hanci daya
Asali: Depositphotos

Dakta Syarifuddin Nasution, babbab likitan sashen haihuwa a yankin Mandailing Natal ya shiadawa jaridar Birtaniya cewar yana zargin wani sinadari dake gurbata iska (Mercury) da kuma wata kwayar cuta (Rubella Virus) a matsayin dalilin haihuwar jaririn cikin wannan yanayi. Sai dai y ace jaririn ba zai wani dade a raye ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel