‘Dalilin da Ya Sa ba Zan Goyi Bayan Tinubu, Atiku Ko Obi ba’: Bulama Bukarti

‘Dalilin da Ya Sa ba Zan Goyi Bayan Tinubu, Atiku Ko Obi ba’: Bulama Bukarti

  • Fitaccen lauya kuma masani kan harkokin tsaro, Bulama Bukarti, ya sanar da shiga siyasar jam’iyya a jihar Yobe
  • Bukarti ya ce ya shafe shekarun ƙuruciyarsa yana fafutukar inganta shugabanci, amma yanzu da ya haura shekara 40
  • Sai dai ya jaddada cewa bai bayyana goyon bayansa ga wasu manyan ’yan siyasar ƙasa ba, ciki har da Tinubu, Atiku da Obi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Damaturu, Yobe - Fitaccen lauya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro, Bulama Bukarti, ya bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar shiga siyasa.

Bukarti ya fadi dalilin barin fafutukar kare muradun jama’a ba tare da shiga siyasar jam’iyya ba, inda ya ce yanzu ya zaɓi shiga harkokin siyasa kai tsaye.

Bukarti ya fadi dalilin shiga siyasa
Shugaba Bola Tinubu da lauya, Bulama Bukarti. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Bulama Bukarti.
Source: Facebook

A hira da ya yi da DCL Hausa, ya ce hakan ya samo asali ne daga burinsa na bayar da gudummawa kai tsaye wajen tafiyar da mulki da maimakon ci gaba da kasancewa mai sharhi a kafafen yaɗa labarai.

Kara karanta wannan

Ciyaman ya yi martani ga Amnesty game da kalaman barazana da ya yi kan zaɓen APC

Bukarti ya goyi bayan gwamnan Yobe, magajinsa

Bukarti ya bayyana goyon bayansa ga Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, da kuma ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2027, Baba Wali.

Ya bayyana cewa bayan shafe yawancin shekarun ƙuruciyarsa yana fafutukar neman shugabanci nagari, ya sake nazarin rayuwarsa lokacin da ya haura shekara 40.

A kalamansa:

“Na yi amfani da ƙarfina na ƙuruciya wajen fafutukar ganin an samu shugabanci nagari, amma yanzu na haura shekara 40. Ba zan iya ci gaba da tafiya a irin wannan hanya ba. Na yanke shawarar shiga siyasa gaba ɗaya domin in bayar da gudummawa bisa fahimtata game da ci gaba.”
Bukarti ya magantu kan shiga siyasa
Lauya kuma dan gwagwarmya a Najeriaya, Bulama Bukarti. Hoto:Bulama Bukarti.
Source: Facebook

Dalilin Bulama na goyon bayan APC

Bukarti ya ce goyon bayan da yake bai wa ’yan siyasar ya samo asali ne daga sanin da yake da su kai tsaye da kuma hulɗarsa da su, ba wai kawai abin da yake karantawa a kafafen yaɗa labarai ba.

Kara karanta wannan

Abin da matasa suka yi wa Dauda Kahutu Rarara a masallacin Abuja ya fusata jigon APC

Ya bayyana cewa fahimtarsa kan gwamna Buni da kuma shirye-shiryen Baba Wali na bunƙasa Yobe ne suka sa ya fito fili ya mara wa shugabannin biyu baya.

Sai dai ya jaddada cewa bai bayyana goyon bayansa ga wasu manyan ’yan siyasar ƙasa ba, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi, saboda bai taɓa haɗuwa da su ido-da-ido ba.

Ya ce:

“Ba zan iya goyon bayan ɗan siyasa bisa abin da na gani a kafafen yaɗa labarai kawai ba. Ban taɓa haɗuwa da Shugaba Bola Tinubu, Peter Obi ko Atiku Abubakar ba. Saboda haka ba zan iya bayyana goyon bayana ga ɗayansu ba.”

Da yake mayar da martani ga masu sukar sauyin matsayinsa daga fafutukar da ba ta nuna goyon bayan wata jam’iyya ba zuwa siyasar jam’iyya, Bukarti ya ce ba za a iya kawo sauyi mai ma’ana ba tare da shiga tsarin gwamnati ba.

Ya yi amfani da wasu ayoyin Alƙur’ani wajen bayyana dalilinsa, inda ya ce rayuwa tana tafiya ne bisa matakai daban-daban, kuma fafutuka ma tana da lokacin da ya kamata mutum ya sauya salon aikinsa.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya magantu kan Rarara, ya fadi yadda Tinubu ya zama masa ala ka kai

A cewarsa:

“Ba za ka iya kawo sauyi daga wajen gwamnati ba. Duk wanda yake tunanin zan ci gaba da fafutuka bayan na haura shekara 40, alhali abokaina da muka yi karatu tare sun zama gwamnoni, ni kuma ina ci gaba da zama mai sharhi a kafafen yaɗa labarai ina sukar su, to ya yi kuskure.”

Bukarti ya ce waɗanda suke son ci gaba da fafutukar kare muradun jama’a har ƙarshen rayuwarsu suna da ’yancin yin hakan, amma shi ba zai nemi afuwa kan sabon matsayinsa na siyasa ba.

Bukarti ya magantu bayan shigowar tawagar Amurka

A wani labarin, an ji cewa Isowar tawagar majalisar dokokin Amurka ya tayar da sabuwar muhawara kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Mai sharhi a kan al'amuran tsaro, Barista Bulama Bukarti ya bayyana cewa bai kamata tawagar ta tsaya a wuri daya ba.

Ya bayyana bukatar ta ziyarci Arewacin Najeriya inda Musulmi da Kirista ke rayuwa a cikin kwanciyar hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.