Jihar Kaduna
Sanata Shehu Sani ya ce harim bam da sojoji suka kai garin Tudun Biri a jihar Kaduna ba kuskure ba ne, ganganci ne da bai kamata ya faru ba. Ya nemi ayi bincike.
A ranar Laraba, 6 ga watan Disamba, masu zanga-zanga sun mamaye majalisar dokokin kasa sannan sun bukaci ministan tsaro, Badaru ya yi murabus kan kisan masu Maulidi.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yu ta'aziyyar mutanen da suka mutu a harin bam din da sojoji suka kai kan masu bikin Maulidi a Kaduna.
Wadanda suka tsira a harin bam da rundunar sojin Najeriya ta kai sun ba da labarin abun da ya faru kan idanunsu. Adadin wadanda suka rasu ya karu zuwa 120.
Kungiyar Dattawan Arewa ta yi martani kan harin bam a Kaduna inda ta ce idan a wata kasa ce da tuni manyan sojojin kasar sun yi murabus kan abin da ya faru.
Hafsan sojin Najeriya, Manjo-Janar Taoreed Lagbaja ya karrama dakaru 86 saboda kwarewar aiki da kuma nuna bajinta a jarabawar karin girma da aka yi musu.
Kungiyar nan mai fafutukar kare hakkin Musulmai MURIC ta buƙaci Gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike mai tsafka kan abin da ya jawo kisan masu maulidi a Kaduna.
Sanatan Kaduna ta kudu, Sunday Marshall Katung, ya ce zai haɗa kai da sauran yan majalisar tarayya na jihar domin kwato hakkin mutanen da aka kashe a Tudun Biri.
Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi Allah wadai da harin bam kan masu Maulidi a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Jihar Kaduna
Samu kari