Shettima da Wasu Jiga-Jigai Sun Dira Kaduna Kan Bama-Baman da Aka jefa Wa Musulmi

Shettima da Wasu Jiga-Jigai Sun Dira Kaduna Kan Bama-Baman da Aka jefa Wa Musulmi

  • Kashim Shettima da wasu manyan kusoshin gwamnati sun ziyarci Kaduna kan harin bama-baman soji a taron masu Maulidi
  • Ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai ziyarci ƙauyen Tudun Biri domin jajantawa waɗanda harin ya shafa
  • Gwamna Uba Sani ne ya tarbi Shettima tare da tawagarsa wadda ta kunshi ministan tsaro, kakakin majalisar wakilai da shugaban APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya isa jihar Kaduna domin jajantawa dangin Musulman da aka kashe a harin bama-baman sojoji.

Shettima ya kawo wannan ziyara ne domin yin ta'aziyya ga dangin waɗanda suka rasu da kuma duba waɗanda suka jikkata sakamakon harin sojoji a kauyen Tudun Biri.

Kara karanta wannan

"Ba ku ci bulus ba" Shugaba Tinubu ya ɗauki mataki mai tsauri kan sojojin da suka jefa bam a Kaduna

Shettima ya ziyarci Kaduna.
Kashim Shettima Ya Sauka a Kaduna Kan Bama-Baman da Sojoji Suka Jefa Wa Musulmi Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Gwamna Malam Uba Sani na jihar Kaduna tare da wasu kusoshin gwamnatinsa ne suka tarbi mataimakin shugaban ƙasan yayin da jirginsa ya sauka a sansanin sojin sama na Mando.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe a wata gajeruwar sanarwa da Gwamna Sani ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Alhamis.

Manyan kusoshin da suka rako Shettima

Jiga-jigan da suka rako mataimakin shugaban ƙasar zuwa Kaduna sun haɗa da kakakin majalisar wakilan tarayya, Tajudeen Abbas, da ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar.

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na cikin tawagar da suka yi wa Shettima rakiya.

Sanarwan ta ce:

"Ba da daɗewa ba Gwamna Uba Sani ya tarbi mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a sansanin rundunar sojin sama da ke Kaduna."
"Mataimakin shugaban ƙasar ya samu rakiyar kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen, ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, da shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje."

Kara karanta wannan

Kus-kus: Ganduje ya shiga ganawar sirri da Gwamna Mai Mala Buni, Ubah da wasu jiga-jigan APC

Dalilin da ya jawo Shettima ya ziyarci Kaduna

Rahotanni sun nuna cewa a farko Shettima ya tsara kai ziyara ƙauyukan da wannan ibtila'i ya shafa ranar Laraba, amma daga bisani ya ɗaga tafiyar zuwa yau Alhamis.

Wannan ziyara na zuwa ne kwanaki huɗu bayan mummunan harin bama-bama da jirgin sojoji ya saki kan masu bikin Maulidi a kauyen Tudun Biri, yankin Igabi.

Tuni dai rundunar sojin ƙasa ta ɗauki laifin cewa jami'anta ne suka kai harin amma ba da gangan ba. Zuwa yanzu dai aƙalla mutane 120 suka rasu.

Barau Jibrin ya aike da sakon ta'aziyya

A wani rahoton na daban Sanata Barau Jibrin ya yi ta'aziyya ga dangin waɗanda harin bam ɗin sojoji ya shafa a kauyen Tudun Biri a jihar Kaduna.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bukaci a gudanar da bincike mai zurfi kamar yadda Bola Tinubu ya bada umarni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel