Tudun Biri: Dattawan Arewa Sun Fadi Abin da Ya Kamata Manyan Sojoji Su Yi, Sun Fadi Dalilansu

Tudun Biri: Dattawan Arewa Sun Fadi Abin da Ya Kamata Manyan Sojoji Su Yi, Sun Fadi Dalilansu

  • Yayin da ake ci gaba da jimamin mutuwar masu Maulidi, kungiya ta bukaci a kori manyan jami'an tsaro
  • Farfesa Yusuf Usman shi ya yi wannan kira inda ya ce da a wata kasa ce da tuni sun yi murabus a karan kansu
  • Wannan na zuwa ne bayan kai harin bam kan masu Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna a ranar Lahadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bukaci manyan shugabannin sojoji da yin ritaya kan kisan masu Maulidi a Kaduna.

A ranar Lahadi ce 3 ga watan Disamba aka kai harin bam kan masu Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Ba za mu yafe ba, Sheikh Jingir ya yi martani kan kisan masu Maulidi a Kaduna, ya tura bukatu

Dattawan Arewa sun bayyana abu da ya kamata manyan sojoji su yi bayan harin bam a Kaduna
Dattawan Arewa sun bukaci Tinubu ya kori manyan sojoji. Hoto: Professor Usman Yusuf.
Asali: Facebook

Wane martani Dattawan Arewa su ka yi?

Mai fashin baki kuma mamban kungiyar, Farfesa Yusuf Usman shi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Abuja, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesan ya ce wannan akwai ganganci a ciki, kuma ya kamata dukkan manyan sojojin a kore su a aiki.

Ya ce ya kamata tun daga kan hafsan tsaron kasar har kasa su yi murabus inda ya ce ya kamata Tinubu ma ya dawo gida da gaggawa.

Ya ce:

"Wannan rashin kwarewa ce, ya kamata dukkan manyan sojojin su yi ritaya ko a kore su.
"Tun daga kan hafsan tsaron Najeriya har zuwa kasa su yi murabus, kuma Tinubu ma ya yanke tafiye-tafiyem da ya ke yi don dawo wa gida Najeriya."

Wace shawara su ka bai wa sojojin?

Ya ce kamata ya yi ace dukkan manyan sojin sun ajiye aikinsu ganin yadda aka shiga jimamin mutuwar wadannan bayin Allah, cewar BusinessDay.

Kara karanta wannan

Ba kuskure ba ne: Ahmad Gumi ya dauki zafi a kan kisan masu taron Maulidi a Kaduna

Farfesan ya koka kan yadda sojoji madadin kare rayukan mutane amma su ke kashe jama'a a kasar.

Har ila yau, hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa da hafsan sojin kasar, Manjo Janar Taoreed Lagbaja sun ziyarci wadanda ke asibiti a jiya Talata 5 ga watan Disamba.

Sojoji sun karrama dakaru 86 kan kwarewar aiki

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta karrama dakarunta 86 saboda nuna kwarewar aiki da kuma bajinta.

Manjo Janar Taoreed Lagbaja, hafsan sojin Najeriya shi ya bayyana haka yayin wani taro a Minna babban birnin jihar Niger.

Asali: Legit.ng

Online view pixel