Sojoji Sun Koma Kashe Fararen Hula: Sanata Sani Ya Ce Babu Kuskure a Harin Kaduna

Sojoji Sun Koma Kashe Fararen Hula: Sanata Sani Ya Ce Babu Kuskure a Harin Kaduna

  • Sanata Shehu Sani ya ce harin bam da sojoji suka kai garin Tudun Biri a jihar Kaduna ba kuskure ba ne, ganganci ne da bai kamata ya faru ba
  • A cewar sanatan, sojoji sun koma kaddamar da hare-hare kan fararen hula amma sun kasa dakile 'yan ta'addan da suka addabi kasar
  • Tsohon sanatan ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da su tabbatar an gudanar da bincike tare da bin kadin jinin bayin Allah da aka zubar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya ya ce babu wani kuskure a harin da bam da sojoji suka kai wa masu maulidi a Tudun Biri, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Yanzu: An nemi ministan tsaron Tinubu ya yi murabus kan kisan masu Maulidi a Kaduna

Sama da mutum 90 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a harim bam din da rundunar soji ta kai garin ranar Lahadi.

Shehu Sani/Jihar Kaduna/Harim Bam/Rundunar Soji
Sanata Shehu Sani ya ce sakim bam da sojoji suka yi kan masu maulidi ba kuskure ba ne, tsabar ganganci ne da bai kamata ya faru ba. Hoto: @ShehuSani
Asali: Twitter

Matsalar tsaro a jihar Kaduna

Rundunar sojin lokacin da ta ke sanar da daukar nauyin sakin bama-baman, ta ce ta yi hakan ne da tunanin 'yan ta'adda ne a garin, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke martani kan harin a hira da Trust TV, Shehu Sani ya bayyana wannan harin matsayin ganganci wanda ya zama wajibi gwamnati ta dauki mataki a kai.

Ya ce:

"Ya kamata mutane su fahimci abin da ya faru a Kaduna ma damar ana batu ne kan tsaro. A shekarun baya, kusan kaso 70 na jihar na fama da matsalar tsaro.
"Kowa ya san rashin tsaro a Kudancin Kaduna wadanda 'yan ta'adda suka addaba. A tsakiyar Kaduna, irinsu Birnin Gwari da Igabi (inda aka kai wannan harin, da karamar hukumar Giwa, duk suna fama da matsalar tsaro."

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Dattawan Arewa sun fadi abin da ya kamata manyan sojoji su yi, sun fadi dalilansu

Sojoji sun koma farmakar fararen hula? - Sanata Sani ya magantu

Shehu Sani ya kuma tariya yadda 'yan bindiga suka farmaki makarantar soji ta NDA, makarantar aikin daji, rukunin gidajen filin jiragen sama duk a jihar.

Ya ce babu wani dan ta'adda da aka taba kamawa ko kashewa a hare-haren da aka kai a jihar.

"Don haka wannan harim bam a Tudun Biri abu ne mai girma wanda aka yi shi kan sakaci. Da farko rundunar ta ce kuskure aka samu, daga baya ta ce wai akwai 'yan ta'adda da ke aiki a wajen.
"Ai akwai dokoki kan farmakar 'yan ta'adda ma damar suka shiga garuruwan fararen hula. Ni ba zan taba gamsuwa da hakan matsayin kuskure ba, ganganci ne wanda idan da dakarun sun bi matakai da hakan ba ta faru ba."

Tsohon sanatan ya ce yanzu ya rage wa gwamnatin tarayya da ta jihar su dauki mataki don kare irin hakan daga faruwa tare da yi wa mutanen da aka kashe musu 'yan uwa adalci.

Kara karanta wannan

Manyan Arewa: Take-taken Tinubu sun nuna bai damu da gyara tsaron Arewa ba

Ya kuma yi nuni da cewa harin da sojojin suka kai Kaduna zai iya zama daya da harin da 'yan bindiga ke kaiwa a fadin kasar la'akari da yadda sojojin suka gaza dakile 'yan ta'addan.

Manyan Arewa: Tinubu bai damu da matsalar tsaron Arewa ba

A wani labarin, kungiyar dattawan Arewa ta caccaki shugaban kasa Bola Tinubu kan mayar da hankali a lamuran tattalin arziki maimakon tsaro a kasar, Legit Hausa ta ruwaito.

Farfesa Usman Yusuf, jigo a kungiyar NEF, ya ce ya zama wajibi Shugaba Tinubu ya kafa kwamiti don bincike kan harin da aka kai jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel