Yanzu: An Nemi Ministan Tsaron Tinubu Ya Yi Murabus Kan Kisan Masu Maulidi a Kaduna

Yanzu: An Nemi Ministan Tsaron Tinubu Ya Yi Murabus Kan Kisan Masu Maulidi a Kaduna

  • Yan Najeriya na ci gaba da yin martani kan kisan Musulmi da rundunar sojin Najeriya ta yi a wajen Maulidi a jihar Kaduna
  • Koda dai rundunar sojin Najeriya ta jaddada cewar kuskure aka samu, sai dai yan Najeriya sun nemi ayi bincike da kyau
  • Sai dai kuma, wasu fusatattun yan Najeriya sun mamaye majalisar dokokin tarayya Abuja, inda suka nemi ministan tsaro ya yi wani abu ko ya yi murabus

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Masu zanga-zanga sun mamaye zauren majalisar dokokin tarayya da ke Abuja a ranar Laraba, 6 ga watan Disamba, kan kisan bayin Allah da dama da jirgin sojoji ya yi a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Dattawan Arewa sun fadi abin da ya kamata manyan sojoji su yi, sun fadi dalilansu

Masu zanga-zangar sun bukaci a yi wa wadanda aka kashe adalci sannan sun nemi ministan tsaro, Abubakar Badaru, da ya tashi ya yi abun da ya rataya a wuyansa ko ya yi murabus, rahoton Daily Trust.

Masu zanga-zanga sun nemi Badaru ya yi murabus
Yanzu: An Nemi Ministan Tsaron Tinubu Ya Yi Murabus Kan Kisan Masu Maulidi a Kaduna Hoto: The National Youth Council of Nigeria, NYCN, Abubakar Badaru
Asali: Facebook

A halin da ake ciki, fiye da mutum 90 ne aka kashe a kauyen Tudun Biri a yankin Rigasa da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna bayan jirgin soji ya jefa bam kan masu bikin maulidi a daren ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna yankin sun ce mutum fiye da 60 ne suka jikkata a harin. Tuni rundunar soji ta dauki alhakin jefa bam din, amma ta ki yin karin bayani.

Da yake jawabi ga manema labarai, jagoran masu zanga-zangar karkashin inuwar kungiyar matasan Najeriya (NYCN) yankin arewa maso yamma, da kungiyar matasan arewa, Nasir Ishaku, ya nemi ayi wa wadanda abun ya ritsa da su adalci, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Haka siddan sojoji suka fara sakar mana bama-bamai, inji wadanda suka tsira cikin masu Maulidi

Ya ce kisan bayin Allah yan Najeriya, musamman a yankin arewacin kasar da ake yawan yi a kullun ba abun yarda bane sannan cewa ba za a sake lamuntan hakan ba.

Ishaku ya bukaci majalisar dokokin tarayya da ta yi bincike kan kisan ranar Lahadi da aka yi a Kaduna sannan ta dauki kwararan mataki domin ceto kasar.

Ya ce:

"Ga wadanda ke da idanun gani, ya kamata su gani da kyau, ga wadanda ke da kunnuwan sauraro, to su ji da kyau. Najeriya bata da lafiya saboda ana kashe yan Najeriya a kullun.
"Yanayin tsaro a kasar na kara tabarbarewa tunda shi (Badaru) ya karbi aiki a matsayin ministan tsaro. Ya wajabta a kan wadannan kungiyoyi biyu su bayyana koke-kokenmu domin Najeriya ta fada halin rugujewa ta fuskar tsaro da rayuka da dukiyoyi, musamman a Arewacin Najeriya.
"Najeriya na ta rasa jami'an rundunar soji da suka hada da na sojin kasa, sojin sama, sojin ruwa da jami'an yan sandan Najeriya. Har yanzu dalibanmu na tsare a hannun masu garkuwa da mutane kuma babu wanda ya san inda suke. Wadannan alamu ne da ke nuna karara cewa ministan ba zai iya rike wannan ma'aikata mai muhimmanci ba. Saboda haka, ya tashi ya yi abun da ya rataya a wuyansa ko ya yi murabus."

Kara karanta wannan

Ba kuskure ba ne: Ahmad Gumi ya dauki zafi a kan kisan masu taron Maulidi a Kaduna

Harin masu Maulidi: Wadanda suka tsira sun magantu

A gefe guda, mun ji cewa mutanen da suka tsira cikin wadanda rundunar sojojin Najeriya ta yi kuskuren sakarwa bam a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, sun bayyana a ranar Talata, 5 ga watan Disamba, cewa sau biyu aka sakar masu bam yayin harin.

Kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto, adadin wadanda suka rasu a wajen ya karu zuwa 120, a cewar jami'an kungiyar Amnesty International, wadanda suka ziyarci yankin a Kaduna don tabbatar da yawan wadanda suka rasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel