Tudun Biri: Kuskure Ne, Babu Bukatar Yin Murabus Na Hafsan Soji Kan Harin Bam, Sanatan Katsina

Tudun Biri: Kuskure Ne, Babu Bukatar Yin Murabus Na Hafsan Soji Kan Harin Bam, Sanatan Katsina

  • Yayin da ake jimamin mutuwar masu Maulidi a Kaduna, Sanata Abdul'aziz Yar'adua ya yi tsokaci kan kiran murabus na hafsan sojin kasar
  • Sanatan wamda ya fito daga jihar Katsina ya bayyana cewa wannan kuskure ne kuma ba ya bukatar sai hafsan sojin ya yi murabus
  • Wannan na zuwa ne bayan kai harin bam kan masu Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Sanata Abdul'aziz Yar'adua ya yi martani game da harin bam kan masu Maulidi a jihar Kaduna.

Yar'adua ya ce wannan harin an samu kuskure ne wanda ba ya bukatar sai hafsan sojoji, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Sojoji sun koma kashe fararen hula: Sanata Sani ya ce babu kuskure a harin Kaduna

Sanata Yar'adua ya yi martani kan kiran murabus na hafsan sojin Najeriya
Sanata Yar'adua ya ce tabbas harin bam kuskure a ka yi a Kaduna. Hoto: Taoreed Lagbaja, Abdul'aziz Yar'adua.
Asali: Facebook

Wane martani Sanatan ya yi kan harin Kaduna?

Sanatan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Laraba 6 ga watan Disamba Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma yabawa hafsan sojin kasar wurin amincewa da kuskuren da su ka aikata inda ya bukaci a kwantar da hankali.

Sanatan ya yi wannan martani ne bayan Kungiyar Dattawan Arewa ta yi kira da manyan shugabannin sojojin da su yi murabus, cewar Daily Post.

Wace shawara Sanatan ya bayar?

Idan ba a mantaba, a ranar Lahadi 3 ga watan Disamba ce sojin kasar su ka jefa bam kan masu Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a Kaduna.

Dan Majalisar ya tabbatar da cewa irin wannan kuskure ba iya rundunar sojin kasar ake samu ba, ko ina ma ana iya samu.

Kara karanta wannan

Yanzu: An nemi ministan tsaron Tinubu ya yi murabus kan kisan masu Maulidi a Kaduna

Ya shawarci gwamnatin jihar Kaduna da ta umarci mutane su rinka sanar da ita duk wani taro makamancin haka don gudun sake afkuwar lamarin.

Dattawan Arewa sun yi martani game da harin bam a Kaduna

A wani labarin, Kungiyar Dattawan Arewa ta yi martani game da harin bam kan masu Maulidi a jihar Kaduna.

Kungiyar ta ce abin da ya kamata shi ne dukkan manyan sojojin kasar su yi murabus.

Wannan na zuwa ne bayan kai harin bam kan masu Maulidi a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.