Kanal Dangiwa: Tsohon Gwamnan Soja Ya Rubuta Wasika ga Tinubu kan Halin da Najeriya ke Ciki

Kanal Dangiwa: Tsohon Gwamnan Soja Ya Rubuta Wasika ga Tinubu kan Halin da Najeriya ke Ciki

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna a mulkin soja, Kanal Abubakar Dangiwa Umar (mai ritaya), ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Shugaba Bola Tinubu
  • Kanal Dangiwa ya yabawa shugaban kasar kan karrama mutanen da suka yi gwagwarmaya don ranar 12 ga watan Yuni
  • Tsohon gwamnan ya tunatar da shugaban kasa abubuwan da ya kamata a ce gwamnatinsa ta mayar da hankali a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kaduna, Kanal Abubakar Dangiwa Umar, ya aika da budaddiyar wasiƙa zuwa ga Shugaba Bola Tinubu.

Kanal Dangiwa ya yaba masa kan karrama gwarazan fafutukar 12 ga watan Yuni, tare da isar da tunatarwa mai ratsa jiki game da alƙawuran da ba a cika ba a tafiyar dimokuradiyyar Najeriya.

Kanal Dangiwa ya ruhuta wasika ga Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Kanal Abubakar Dangiwa Umar (mai ritaya) Hoto: Bayo Onanuga, Shehu Sani
Source: Facebook

Kanal Dangiwa ya aika wasika ga Tinubu

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yi magana kan beli 'mai tsauri' da aka saka wa El Rufa'i

Jaridar Premium Times ta kawo rahoton fitar da wasikar da tsohon gwamnan ya yi a ranar Laraba, 17 ga watan Yunin 2026.

A cikin wasiƙar, Kanal Dangiwa ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasar saboda fitowa fili ya amince da jami'an soja da fararen hula da suka sanya rayuwarsu cikin haɗari domin yaƙar soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yuni, 1993.

Dangiwa ya bukaci a kawo gyara

Sai dai, Kanal Dangiwa, wanda tsohon kanal ne mai ritaya, cikin hanzari ya sauya akalar kalaman yabon zuwa tsauraran bita kan yanayin da ƙasar take ciki a halin yanzu.

Tsohon gwamnan ya buƙaci gwamnatin da ta gaggauta magance matsalolin gaggawa na ƙasa, musamman rashin tsaro da talauci, jaridar Solacebace ta kawo rahoton.

"Zuwa ga sbugaban kasa"
"Godiya kan amincewa da ayyukan da jami'an rundunar sojojin Najeriya suka yi wa dimokuradiyya a lokacin fafutukar 12 ga Yuni."
"Ina mai mika gagarumar godiyata kan yadda ka fito fili ka amince da ayyukan da wasu jami'an rundunar sojojin Najeriya suka yi, waɗanda aka karanta sunayensu a lokacin jawabin ranar dimokuradiyya a ranar 12 ga watan Yuni, 2026."

Kara karanta wannan

'Zabe ne a gabansa': Yan majalisa sun dura kan Tinubu game da tsaron ƙasa

"Wannan batu ya kasance ɓangare na batutuwan da ke cikin bayanin da na yi wa jama'a a makamancin wannan lokaci a shekarar da ta gabata."
"Hakika ya dace kuma ya kamata a fito fili a karrama 'yan ƙasa da suka sanya rayuwarsu a hadari a cikin fafutukar gyara zaluncin soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yuni, 1993."
"Dole ne kuma na gode maka da ka karrama sauran gwaraza fararen hula da aka ambata a cikin jawabin naka, waɗanda suka yi sadaukarwa daban-daban domin ganin an soke wannan haramtaccen soke zaɓe."
"Abu ne mai wahala a zurfafa cikin wannan gaskiya, shugaban kasa, cewa 12 ga watan Yuni wani gagarumin lokaci ne a fafutukarmu ta zuwa dimokuradiyya, kuma bikin tunawa da shi na shekara-shekara ya dace ƙwarai da gaske."
"Duk da haka, saboda wannan taro ne na shekara-shekara, na tabbata sauran mutane, na soja, na fararen hula, masu rai ko waɗanda ba sa raye, waɗanda suka cancanci irin wannan karramawa amma ba su samu ba tukuna, za a gano su kuma a karrama su a daidai lokacin da ya dace."

Kara karanta wannan

1448AH: Tinubu ya taya musulmi murna, ya tabo hijirar Annabi SAW daga Makkah zuwa Madina

"Abin da waɗannan jami'ai suka hango lokacin da suka sanya rayuwarsu a cikin hadari tun a shekarar 1993, ya kasance, don amfani da kalmar da ta fi dacewa, babban buri ne."
"Hasali ma sun ɗauki tsaron 'yan ƙasarmu a matsayin tabbataccen abu; babban dalilin wanzuwa, mafi ƙarancin sharadi na kasancewar kowace gwamnati, na dimokuradiyya ko akasin haka. Idan babu tsaron ƙasa, wannan shi ne ƙarshen magana; babu wani abu daban da zai yi amfani. Babu ko ɗaya!"
"Kuma, yayin da muke kan wannan, shugaban kasa, ka ba ni damar tunatar da kai game da abin da kuma ya ƙarfafa gwiwar jami'an a can baya."
Sun yi marmarin dimokuradiyya da ta haɗa da mafi muhimman siffofinta; rabe-raben madafun iko, fannin shari'a mai zaman kansa kuma maras son zuciya wanda zai bayar da adalci ba tare da gurɓata shi da ra'ayin bangaranci ba."
"Hukumar zaɓe mai zaman kanta da gaske wadda ke tabbatar da zaɓe na gaskiya da adalci, manufofin tattalin arziki da ke kare jin daɗin 'yan ƙasa da kuma yawan aiki."
"Sun kuma dora fatansu a kan gagarumin yaƙi da talauci, musamman a tsakanin talakawan da ke ƙasan rukunin al'umma."

Kara karanta wannan

Ran shugaban gwamnonin Arewa ya baci kan surutu babu aiki, ya kawo mafita

"Shugaban kasa, a matsayinka na wanda ya daɗe yana fafutukar tabbatar da gaskiya, daidaito, adalci da kuma tafiya da kowa, da yawa daga cikinmu ba mu ga dalilin shakkar alƙawarinka na samar da kyakkyawar makoma da sabon fata ga dukkan 'yan Najeriya kamar yadda aka tsara a babi na biyu na tsarin mulkinmu ba."
"Don haka, domin kada sadaukarwar da waɗannan jami'ai da sauran 'yan Najeriya suka yi wajen cimma fafutukar 12 ga watan Yuni ta tafi a banza, ina ba da shawarar cewa waɗannan manufofi su sake zama tushen manufofinka na ƙasa." -

Kanal Abubakar Dangiwa Umar

Kanal Dangiwa ya ba Shugaba Tinubu shawara
Kanal Abubakar Dangiwa Umar tare da Sanata Shehu Sani Hoto: Shehu Sani
Source: Facebook

'Yan majalisa sun soki Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa bangaren marasa rinjaye na majalisar wakilai, ya ragargaji shugaban kasa Bola Tinubu kan rashin tsaro.

Mambobin na majalisar wakilai sun zargi gwamnatin tarayya da sakaci da mayar da hankali kan babban zaɓen shekarar 2027.

Sun nuna takaici kan kisan Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya wanda aka ce an sace shi tare da matarsa a Katsina kafin daga baya aka sanar da mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng