Sanusi II Ya Yi Maganar Kisan Masu Maulidi, Ya Fadi Nasarar Farko Da Aka Samu

Sanusi II Ya Yi Maganar Kisan Masu Maulidi, Ya Fadi Nasarar Farko Da Aka Samu

  • Muhammadu Sanusi II ya aiko da sakon ta’aziyya ga musulman da sojoji su ka kashe da bam-bamai a garin Kaduna
  • Sarkin Kano na 14 ya kira lamarin da abin takaici, ya kuma ji dadin yadda masu laifi su ka amsa laifin da su ka aikata
  • Sanusi II ya roki Allah SWT ya amsa shahadar wadanda aka kashe a lokacin da su ke tsakiyar Maulidin Annabi SAW

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Muhammadu Sanusi II ya aiko ta sakon ta’aziyya ga mutanen Tudun Biri a sakamakon rashin da su ka yi a karshen makon jiya.

Sarkin Kano na 14 ya fitar da ta’aziyyar ne a shafin Twitter kamar yadda Legit ta fahimta.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Hanyoyi 5 Sojoji Za Su Bi a Kiyaye Kashe Bayin Allah – Farfesa Pantami

Sanusi da masu maulidi
Sanusi II ya yi ta'aziyyar kashe masu maulidi Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Twitter

Sanusi: Inna lilLahi wa Inna ilayhi raji'un

Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya fara da ‘Inna lilLahi wa Inna ilayhi raji'un, yake cewa dukkan wani mai rai zai komawa Allah SWT.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Khalifan na Tijjaniyya a Najeriya yake cewa ya ji takaicin samun labarin masifar da ta aukawa Bayin Allah musulmai a wajen taron maulidi.

Sanusi II ya ce kashe mutane da kuma raunata dinbin jama’a da dakarun sojoji su ka yi da sunan kuskure, ya girgiza daukacin al’ummar kasar.

"Sojoji sun amsa laifinsu" - Sanusi II

Tun da har sojoji sun amsa laifisu, Mai Martaban ya ce an fara cin ma nasara wajen shawo kan wannan matsalar da ta ke maimaita kan ta.

A cewar Khalifa, a lokutan baya sai irin haka ta faru, amma kuma kowa ya zare hannunsa. Duk da haka an ji shi a bidiyo ya ce ayi bincike.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisan da aka Yi tun 1992 sun tuno tsohon bashin da su ke bin Gwamnati

Bangaren jawabin Mai martaba Muhammadu Sanusi II

"Akwai sauki idan aka lura da cewa jami’an sojoji sun karbi laifin wannan lamari.
An samu cigaba daga abin da aka saba a gwamnatocin baya inda ake nuna halin rashin tausayi da kin daukar laifi.
Mun kuma lura gwamnatin Kaduna ta na aiki da hukumomi domin taimakawa wadanda su ka samu rauni tare da tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa.
A madadin daukacin ‘yan darikar Tijjaniyya a Najeriya, ina aika ta’aziyyar duka wadanda aka easa, ina fatan Allah ya karbi shahadarsu.
Sannan ina addu’ar samun lafiya ga wadanda su ka samu rauni."

Zanga-zanga a kan kashe mutanen Kaduna

Ana tsakiyar maulidi a kauyen Tudun Biri, aka ji labari sojojin Najeriya sun harba bama-bamai ga Bayin Allah, hakan ya jawo zanga-zanga.

Abin da ya faru a karamar hukumar ta Igabi ya sa jama’a sun yi tir da yadda ake kashe yawan mutanen da ba su san hawa ko sauka a Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel