Yayin da Ake Jimamin Mutuwar Masu Maulidi, Rundunar Soji Ta Karrama Sojoji 86, Ta Fadi Dalili

Yayin da Ake Jimamin Mutuwar Masu Maulidi, Rundunar Soji Ta Karrama Sojoji 86, Ta Fadi Dalili

  • Yayin da ake jimamin mutuwar mutane da dama a harin bam kan masu Maulidi, rundunar sojin ta karrama wasu
  • Hafsan sojin Najeriya, Manjo Janar Taoreed Lagbaja shi ya bayyana haka yayin kaddamar da gidajen kwanan manyan sojoji a Minna
  • Ya hori sojojin 86 da su ka samu karin girma da su kara kaimi wurin tabbatar da samun nasara da aiki cikin natsuwa da kuma kwarewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - Hafsan sojin Najeriya, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya bukaci sojoji da su yi aiki da kwarewa don ci gaba da daukaka kasar Najeriya a idon duniya.

Lagbaja ya bayyana haka ne yayin kaddamar da gidajen Burgediya Janar da Manjo Janar da kuma karramawa a Minna da ke jihar Niger.

Kara karanta wannan

Ba kuskure ba ne: Ahmad Gumi ya dauki zafi a kan kisan masu taron Maulidi a Kaduna

Rundunar sojin Najeriya ta karrama dakarunta 86 saboda kwarewar aiki
Rundunar soji ta karrama sojoji 86 yayin da ake jimami a Kaduna. Hoto: Nigerian Army.
Asali: Twitter

Mene dalilin karrama sojojin da aka yi a Niger?

Hafsan sojin wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Sani Gambo ya ce sojoji akalla 86 ne za a karrama a yayin bikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sojojin sun kasance gwaraza a jarrabawar karin girma da aka yi a wannan shekara ta 2023, cewar Daily Trust.

Gambo ya ce an ba da kyaututtukan ne don karfafa musu gwiwa da kuma zama abin koyi ga na kasa da su.

Wane shawara sojojin da aka karrama su ka samu?

Tun farko a martaninshi, kwamanadan horaswa na rundunar, Manjo Janar K. O Aligbe ya ce sojojin sun ware kansu inda su ka yi bajinta a yayin jarabawar da aka gudanar.

Aligbe ya bukace su da su ci gaba da daga kansu sama kamar yadda su ka yi a yanzu don ganin sun inganta aikinsu yadda ake so, cewar Voice of Nigeria.

Kara karanta wannan

Harin bam a Kaduna: Mun yi takaici, shugaban sojoji ya roki afuwa kan kisan mutum 85

Ya ce yayin da sojojin ke ci gaba a bangarorin ayyukansu, su na rubuta jarrabawar karin girma don samun ci gaba.

Sojoji sun kare matakin harin bam a Kaduna

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta kare matakin kai harin bam kan masu Maulidi a Kaduna a ranar Lahadi.

Lamarin ya faru ne a Lahadi 3 ga watan Disamba da dare a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel