Ba Kuskure Ba Ne: Ahmad Gumi Ya Dauki Zafi a Kan Kisan Masu Taron Maulidi a Kaduna

Ba Kuskure Ba Ne: Ahmad Gumi Ya Dauki Zafi a Kan Kisan Masu Taron Maulidi a Kaduna

  • Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya soki dakarun sojoji bayan samun labarin bam ya kashe mutane a kauyen Tudun Biri
  • Malamin musuluncin da ke zama a garin Kaduna yana ganin abin da ya faru ba kuskure ba ne kamar yadda ake fada
  • Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya aika sakon ta’aziyya, kuma ya bada shawarar a biya diyyar rayuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi tir da abin da ya faru a garin Tudun Biri da sojoji su ka kashe Bayin Allah kusan 100.

A wani jawabi da ya fitar a Facebook, Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya kira lamarin da abin takaici da ke faruwa a yankin Arewa.

Kara karanta wannan

Yanzu: An nemi ministan tsaron Tinubu ya yi murabus kan kisan masu Maulidi a Kaduna

Gumi.
Shehin malamin musulunci Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

Shehin yake cewa ana maida jihohin Arewacin Najeriya tamkar zirin Gaza inda sojojin Israila su ke hallaka mutanen kasar Falasdin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin addinin ya zargi hukumomi da mugun nufi da kuma yin kisan kare dangi da ganganci ga al’ummar da ke kauyukan Arewa.

"Ba za ta yiwu ayi kuskure wajen harba bam ga masu fararen kaya ba. Ana amfani da bam ne a kan sa’o’in dakarun abokan fada.
Ba za a yarda da wannan ba, abin Allah-wadai ne kuma akwai wata kullaliya."

- Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud

Masanin ilmin fikihun yake cewa makiyaya su na kukan ana kashe su babu gaira babu dalili, ana harba bama-bamai a rugagensu.

Gumi ya kara maganarsa da cewa ana fuskantar matsala a yadda ake fama da rashin sanin ya kamata, yana nuni ga sojoji da hukuma.

Kara karanta wannan

Harin bam a Kaduna: Mun yi takaici, shugaban sojoji ya roki afuwa kan kisan mutum 85

Dr. Rijiyar Lemu ya yi tir da kisan Kaduna

A ranar Talata kuma Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi magana a kan abin da ya faru, ya kuma jajantawa al’umma.

Bayan haka, Farfesan ya bada wasu shawarwari ga mahukunta tun daga fara bincike tare da biyan diyyar duk wadanda aka rasa a harin.

Kisan Jama’a a Kaduna: Ta’aziyya Da Jan hankali Ga Mahukunta:

1. Muna mika ta’aziyyar mu da duk yan’uwa da abokan arzuki da ilahirin Musulmin Nijerya bisa ga abin bakin cikin da ya faru ranar Lahadi da ta gabata, na harin da ake zargin jirgin yakin sojojin Nijeriya ya kai wa wasu Musulmi a Kaduna, wanda ya jayo asarar rayuwa masu yawa, baya ga wadanda aka ji wa raunuka. Muna addu’a Allah ya gafarta musu, ya sanya Aljanna ce makomarsu.
2. Sannan muna kira ga mahukunta cewa, lalle su gudanar da bincike a kan dalilan faruwar irin wannan aika-aika da wadanda suke da hannu a ciki, da daukan kwakkwaran mataki da zai dakatar da ci gaba da faruwar hakan a nan gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnati Za Ta Biya Diyyar Mutane 85 da Sojoji Su Ka Kashe da Bam a Kaduna

3. Sannan lalle wajibi Gwamnati ta biya diyyar wadanda suka rasa rayukwansu da kuma wadanda aka ji wa raunuka.
4. Allah ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa a kasarmu da sauran kasashen Musulmi baki daya. Amin.

- Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu

Sani Rijiyar Lemu a kan juyin mulkin Nijar

Ana da labari Sheikh Muhammad Sani Rijiyar Lemu ya yi magana mai jan hankali kan juyin mulkin da aka yi a Nijar kwanakin baya.

Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemu ya ba shugaba Bola Tinubu shawara cewa ka da ya ɗauki matakin bindiga a kan makwabtan Najeriyan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel