Haka Siddan Sojoji Suka Fara Sakar Mana Bama-Bamai, Inji Wadanda Suka Tsira Cikin Masu Maulidi

Haka Siddan Sojoji Suka Fara Sakar Mana Bama-Bamai, Inji Wadanda Suka Tsira Cikin Masu Maulidi

  • Wadanda suka tsira a harin Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna sun bayyana halin da suka shiga, cewa sau biyu aka yi masu ruwan bama-bamai
  • Hakan na zuwa ne yayin da adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 120, kamar yadda jami'an Amnesty International da suka ziyarci yankin suka bayyana
  • A ranar Lahadi, rundunar soji sun yi kuskuren daukar masu Mauludi da suka taru a matsayin yan bindiga a kokarinsu na raba yankin da kungiyar yan ta'adda

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Igabi, Kaduna - Mutanen da suka tsira cikin wadanda rundunar sojojin Najeriya ta yi kuskuren sakarwa bam a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, sun bayyana a ranar Talata, 5 ga watan Disamba, cewa sau biyu aka sakar masu bam yayin harin.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Sanata ya faɗi matakin da zasu ɗauka domin tabbatar da adalci kan kisan masu Maulidi

Kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto, adadin wadanda suka rasu a wajen ya karu zuwa 120, a cewar jami'an kungiyar Amnesty International, wadanda suka ziyarci yankin a Kaduna don tabbatar da yawan wadanda suka rasu.

Shugaban hafsan soji ya ziyarci Tudun Biri
Haka Siddan Sojoji Suka Fara Sakar Mana Bama-Bamai, Inji Wadanda Suka Tsira Cikin Masu Maulidi Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Jirgin yakin sojoji ya kashe yan farar hula bisa kuskure a Kaduna

Jirgin yakin sojin ya yi nufin kakkabe yan ta'adda ne a daren ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, amma sai ya dira kan yan farar hula da ke bikin maulidi a Tudun Biri bisa kuskure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar sojin ta dauki alhakin lamarin, sannan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayyana adadin wadanda suka mutu a matsayin 85. NEMA ta kara da cewar mutum 66 ne suka jikkata.

Sai dai a ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba, kungiyar dattawan arewa, ta Jama'atu Nasril Islam, da na yan siyasar arewa sun yi watsi da harin, suna masu kira da a hukunta wadanda aka samu da laifi.

Kara karanta wannan

Harin bam a Kaduna: Mun yi takaici, shugaban sojoji ya roki afuwa kan kisan mutum 85

Mazauna kauyen Kaduna sun ba da labarin harin

Saudatu Alamagani, mai shekaru 45, ta bayyanawa manema labarai cewa sau biyu rundunar sojin Najeriya ta sakarwa kauyen bama-bamai.

A cewarta, ta tsallake rijiya da baya ne da har bama-baman basu kashe ta ba, tana mai cewa da farko abun ya yi kama da shirin wasan kwaikwayo lokacin da ya fara da misalin karfe 10:00 na dare lokacin da Musulmai ke bikin maulidi sannan ana sakar masu bama-bamai.

"Sojojin sun fara yi mana ruwan bama-bamai", inji ta, tana mai karawa da cewar taron sun zata yan bindiga ne ke sakar bama-baman.

Ta kara da cewar gawarwaki sun bazu a ko'ina yayin da mutane ke gudun neman tsira, rahoton Vanguard.

Alamagani ta bayyana cewa lokacin da wasu yan garin suka tafi neman yan acaba da za su kwashi wadanda suka jikkata zuwa asibiti don samun kulawar likitoci, sai sojojin suka sake sakin bam.

Kara karanta wannan

Izala ta yi Allah wadai da kisan masu bikin Maulidi a Kaduna, ta tura sako

MURIC ta magantu kan kisan masu Maulidi

A wani labarin, mun ji cewa kungiyar nan mai fafutukar kare hakkin musulmai a Najeriya 'Muslim Rights Concern (MURIC)' ta maida martani kan bama-baman da sojoji suka jefa wa masu Maulidi a Kaduna.

Kungiyar ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta hanzarta gudanar da bincike kan harin bama-baman jirgin soji, wanda ya halaka Musulmai aƙalla 120 a kauyen Tudun Biri.

Shugaban MURIC na ƙasa, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel