Zaben Ekiti: Dan Takarar Gwamnan ADC Ya Sha Kaye, APC Ta Yi Nasara a Rumfarsa
- Yayin da ake ci gaba da zaben gwamna, jam'iyyar APC ta yi nasara a mazabar dan takarar gwamna a ADC a zaben jihar Ekiti
- APC ta doke ɗan takarar ADC, Ambasada Dare Bejide, a rumfarsa ta zaɓe da ke Ilawe-Ekiti, inda APC ta samu ƙuri’u 140
- An samu rahotannin tashin hankali da yunƙurin sayen ƙuri’u a rumfar zaɓen Bejide, amma jami’an tsaro sun shawo kan lamarin cikin nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ekiti - Ana ci gaba da samun sakamakon zaben jihar Ekiti da ake gudanarwa a yau Asabar 20 ga watan Yunin 2026.
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a zaɓen Ekiti, Ambasada Dare Bejide, ya sha kaye a rumfarsa ta zaɓe a hannun ɗan takarar APC kuma gwamna mai ci, Biodun Abayomi Oyebanji.

Kara karanta wannan
Ekiti 2026: Rigima mai zafi ta kaure tsakanin magoya bayan APC da ADC bayan an jibge kudi

Source: Facebook
An samu matsala a wasu rumfunan zabe
Rahotanni sun nuna cewa an samu ɗan tashin hankali da kuma yunƙurin sayen ƙuri’u a Rumfa ta 4, Gunduma ta 2, ƙaramar hukumar Ekiti Ta Kudu maso Yamma da ke Ilawe-Ekiti, cewar The Nation.
Sai dai jami’an tsaro sun yi gaggawar shiga tsakani, lamarin da ya taimaka wajen hana matsalar ta ƙara kamari yayin gudanar da zaɓen.
Kwamishinan ’yan sanda mai kula da zaɓen, CP Abayomi Shogunle, wanda ya kai ziyara wurin, ya ce komai na tafiya yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa ƙananan saɓanin da aka samu ba sabon abu ba ne a irin manyan zaɓukan da ake fafatawa da ƙarfi.
Sakamakon farko daga rumfar ya nuna cewa jam'iyyar APC ta samu ƙuri’u 140, yayin da ADC ta samu ƙuri’u 37 kacal.
Jam’iyyar AAC ta samu ƙuri’u biyu, PDP ta samu ƙuri’a ɗaya, sannan APGA da ADP suka samu ƙuri’a ɗaya-ɗaya.
Haka kuma, a Rumfa ta 7, Gunduma ta 1 a yankin Ilupe, APC ta samu ƙuri’u 70 yayin da ADC ta samu 15.

Source: Twitter
Yadda aka sanar da wasu sakamakon zaben Ekiti
A Rumfa ta 12, Gunduma ta 1 da ke Owaosun/Tedio, APC ta samu ƙuri’u 57, ADC ta samu 10, PDP ta samu huɗu.
Jam’iyyar ADP kuma ta samu ƙuri’a ɗaya a wannan rumfa, kamar yadda sakamakon farko ya nuna.
A Rumfa ta 1, Gunduma ta 1 cikin Makarantar Katolika ta St Angela, APC ta samu ƙuri’u 88, cewar rahoton Daily Post.
PDP ta samu ƙuri’u 14, ADC ta samu huɗu, yayin da aka soke ƙuri’u tara saboda wasu kura-kurai.
Zaben Ekiti: An kona ofishin yan sanda
Kun ji cewa tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya yi Allah-wadai kan kona ofishin ‘yan sanda yayin da ake zaben gwamna a jihar.
Fayemi ya yaba wa hukumar zabe kan yadda tantance masu kaɗa ƙuri’a ta gudana cikin sauƙi da tsari, tare da bayyana aikin a matsayin nasara.
Ya buƙaci mazauna Ekiti su ci gaba da zaman lafiya, yana mai cewa al’ummar Isan-Ekiti masu son zaman lafiya ne duk da abin da ya faru.
Asali: Legit.ng
