Ba Za Mu Yafe Ba, Sheikh Jingir Ya Yi Martani Kan Kisan Masu Maulidi a Kaduna, Ya Tura Bukatu

Ba Za Mu Yafe Ba, Sheikh Jingir Ya Yi Martani Kan Kisan Masu Maulidi a Kaduna, Ya Tura Bukatu

  • Kungiyar Izala karkashin jagorancin Sheikh Sani Yahaya Jingir ta yi Allah wadai da harin bam ka masu Maulidi a Kaduna
  • Kungiyar ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi gaggawar yin bincike don zakulo wadanda su ka yi wannan aika-aika tare da hukunta su
  • Shugaban kungiyar, Sheikh Sani Yahaya Jingir shi ya bayyana haka a gidansa da ke birnin Jos yayin ganawa da manema labarai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Shugaban Majalisar Malamai ta Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi Allah wadai da kisan masu Maulidi a Kaduna.

Sheikh Jingir ya ce kada gwamnati ta ce a bar wa Allah kisan da akayi inda ya ce Allah da kansa ya haramta kisa.

Kara karanta wannan

Izala ta yi Allah wadai da kisan masu bikin Maulidi a Kaduna, ta tura sako

Sheikh Jingir ya yi martani game da harin bam kan masu Maulidi a Kaduna
Izalar Jos ta yi Allah wadai da harin bam kan masu Maulidi a Kaduna. Hoto: Sheikh Sani Yahaya Jingir.
Asali: Facebook

Mene martanin Sheikh Jingir kan kisan?

Shehin Malamin ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi kwakkwaran bincike don binciko wadanda ke da hannu a kai harin, cewar Aminiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ba za su taba amincewa da wannan kisan gilla ba da aka yi wa 'yan uwa Musulmai don haka bai kamata a bari ya tafi a banza ba.

Ya ce:

"A hukunta duk wanda aka samu da hanu a wannan kai hari, kada gwamnati ta ce a bar wa Allah.
"Domin Allah da kansa ya yi umarnin a hukunta duk wanda ya aikata irin wannan al’amari."

Wane martani Jingir ya yi kan kisan?

Jagoran kungiyar ta bayyana haka ne a wani taron ganawa da 'yan jaridu da ya kira jiya a gidansa da ke birnin Jos a jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Gwamnati Za Ta Biya Diyyar Mutane 85 da Sojoji Su Ka Kashe da Bam a Kaduna

Sheikh Jingir ya ce aikin ko wane irin shugaba ne ya kare rayukan al’ummar da ya ke yiwa Shugabanci.

Ya kara da cewa:

"Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin bincike, wanda zai binciko ainihin abin da ya faru kan wannan hari da aka kai."

Izala ta yi Allah wadai da harin Kaduna

A wani labarin, Kungiyar Izala karkashin jagorancin Sheikh Bala Lau ta yi Allah wadai da harin bam kan masu Maulidi a jihar Kaduna.

Sheikh Bala Lau shi ya bayyana haka a jiya Talata 5 ga watan Disamba inda ya bukaci gwamnati ta yi bincike don hukunta masu laifi.

Ya ce abin takaici ne yadda aka harba bam kan 'yan uwa Musulmai inda ya yi musu addu'ar samun rahama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel