Matar Shugaban Izala a Kano, Sheikh Abdullahi Pakistan Ta Rasu

Matar Shugaban Izala a Kano, Sheikh Abdullahi Pakistan Ta Rasu

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Kano sun bayyana cewa matar tsohon shugaban hukumar alhazai ta kasa, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan ta rasu
  • Wani daga cikin na kusa da Sheikh Pakistan ya bayyana cewa Hajiya Zainab da ta rasu ta shafe lokaci tana fama da rashin lafiya mai matukar tsanani
  • Biyo bayan tabbatar da rasuwar Hajiya Zainab, an sanar da lokaci da wajen da za a yi mata jana'iza a yau Asabar, 20 ga Yunin shekarar 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - An tabbatar da rasuwar matar shugaban Izala na jihar Kano kuma tsohon shugaban hukumar NAHCON, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan.

Rahotanni sun nuna cewa matar malamin mai suna Hajiya Zainab ta rasu ne a daren Juma'a, 19 watan Yunin shekarar 2026.

Kara karanta wannan

An fallasa shirin shawo kan talaka da shinkafa da taliya a zaben gwamnan Ekiti

Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan
Sheikh Abdullahi Pakistan yayin hira da 'yan jarida. Hoto: Abdullahi Suraj Nagegime
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa daya daga cikin hadiman Sheikh Pakistan, Abdullahi Suraj Nagegime ne ya fitar da sanarwa game da rasuwar Hajiya Zainab a Facebook.

Matar Sheikh Abdullahi Pakistan ta rasu

Sanarwar da Abdullahi Suraj Nagegime ya fitar ta nuna cewa an fara shirye-shiryen jana'izar marigayiya matatar Sheikh Pakistan a yau.

A daren jiya Juma'a, ya wallafa cewa:

"​Allah ya yi wa matar Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan rasuwa, Hajiya Zainab, a cikin daren nan na Juma'a 19/06/2026.
​"Marigayiyar, Hajiya Zainab, ta dade tana fama da jinya, muna addu'ar Allah ya sanya wannan jinyar ta zama kaffara a gare ta."

Game da jana'iza, ya ce:​

"In sha Allah, za a gabatar da jana'izarta da safe da misalin karfe 10:00.
"​Muna addu'ar Allah ya jikanta da rahama, ya sanya aljanna ce makomarta, ya kuma ba Farfesa Pakistan hakurin rashin da ya yi. Amin."
Sheikh Abdulahi Saleh Pakistan
Sheikh Abdullahi Pakistan a ofis din NAHCON kafin murabus. Hoto: NAHCON
Source: Facebook

Matatar Pakistan ta yi jinya kafin mutuwa

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yi magana kan beli 'mai tsauri' da aka saka wa El Rufa'i

Abdullahi Suraj ya bayyana cewa marigayiyar ta shafe tsawon lokaci tana fama da rashin lafiya, wanda ya kai ga kwantar da ita a asibiti.

Ya ba da labarin rashin lafiyar da ta yi yana cewa:

"Sallar azumi a gadon asibiti ta yi, hakama babbar sallah a kan gadon asibiti ta yi.
"Tun sallar azumi take kwance babu lafiya, haka a wannan sallar ta babbar sallah, ranar sallah jikin nata ya kara tsananta sosai muka fito ita daga daki za a kai ta asibiti.
"Mun fito da ita lokacin da zamu tafi asibiti mun zo kofar dakin ta sai tace; to yan uwa a yafe mu mu dai mun tafi ba mu sani ba ko zamu dawo.
"Tana gama maganar nan naji kwalla sun cika ido na muka ce in shaa Allah za ki samu sauki ki dawo gida."

Shugaban Izala ya rasu a Kebbi

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Izala na karamar hukumar Besse a jihar Kebbi, Malam Yahaya Balli ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya

Shugaban Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa rashin Malam Yahaya ya shafi kasa baki daya ba Kebbi kadai ba.

Bayan mika sakon ta'aziyya ga iyalai, 'yan uwa da abokan arziki, Bala Lau ya bukaci limamai su kara dagewa da addu'ar neman zaman lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng