Jama’a Sun Jero Bukatunsu Wajen Zanga Zanga a Kaduna a Dalilin Kashe 'Yan Maulidi

Jama’a Sun Jero Bukatunsu Wajen Zanga Zanga a Kaduna a Dalilin Kashe 'Yan Maulidi

  • Jama’a sun cigaba da nuna takaicinsu a kan yadda sojoji su ka harba bama-bamai ga mutanen da ke taron addini
  • Kisan jama’a da aka yi a Tudun Biri a jihar Kaduna ya jawo an gudanar da zanga-zanga a birnin Abuja da Zariya
  • Masu zanga-zangar sun gabatar da bukatunsu ga gwamnati, sun nemi a kawo karshen abin da aka kira kuskure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Zanga-zanga ta barke a wasu wuraren a sakamakon kashe mutane da rundunar sojojin kasa su ka yi a Tudun Biri a Kaduna.

Legit ta samu labari cewa wasu mutane sun shirya zanga-zanga a garin Zariya da ke jihar Kaduna domin nuna fushinsu kan abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi zanga zanga a Majalisa, sun ce Minista ya sauka bayan tono laifuffukansa

Tudun Biri
'Yan Maulidi da aka kashe a Tudun Biri Hoto: HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Zanga-zanga a Abuja da Zariya

Kamar yadda aka yi a birnin tarayya Abuja, masu zangar sun yi kira ga hukumomi cewa bai kamata irin haka ta sake faruwa nan gaba ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sahara Repoters ta ce masu zanga-zangar lumanar sun fito suna cewa “Ayi wa Arewa adalci”, “Ayi wa Igabi adalci” ko “A kare Arewa!”

Musulunci ya yarda da zanga-zanga?

Zanga-zangar ta zo ne yayin da jama’a su ka rabu biyu inda wasu su ke ganin bai halatta a fito ayi wa gwamnati zanga-zanga a musulunci ba.

Wasu kuma suna ganin babu inda addini ya hana zanga-zangar lumunar da ba bore ba.

Daily Trust ta ce bayan wadanda su ka yi zanga-zanga a Zariya, kungiyar NSGF ta gwamnonin Arewa ta yi Allah-wadai da kisan da aka yi.

Abin da mutanen Kaduna su ka bukata?

Kara karanta wannan

Yanzu: An nemi ministan tsaron Tinubu ya yi murabus kan kisan masu Maulidi a Kaduna

Saleem Yunusa wanda yana cikin wadanda su ka yi wannan zanga-zanga a garin Zariya a ranar Laraba, ya samu yin jawabi a wajen.

Malam Saleem Yunusa ya ce abin da su ke nema shi ne hukunta wadanda ke da hannu wajen kashe mutane da aka yi da sunan kuskure.

Matashin ya bukaci a biya cikakkiyar diyya ga iyalan da aka kashe sannan ayi hattara domin ganin ba a sake maimaita haka a gaba ba.

Zanga-zangar Wike a Abuja

Labari ya zo cewa kungiyoyi masu zaman kan su da wasu mutane sun hurowa Nyesom Wike a birnin Abuja inda su ka yi zanga-zanga a majalisa.

An zargi Ministan harkokin Abuja da kawo munanan tsare-tsare da karbe filayen mutane don haka aka bukaci ya sauka daga kujerar da yake kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel