Jihar Kano
Kungiyar ‘yan kasuwar 'Singer' a jihar Kano ta roƙi Aliko Dangote da mai kamfanin BUA su rage farashin sukari kafin Ramadan don rage wa talakawa wahala.
Sheikh Muhammad Bin Usman zai koma limanci a masallacin Kundila na Sahaba bayan rikici da aka yi a masallacin Jami'urrahma. Sheikh Ibrahim Kalil ne ya sanar da haka.
Sanata Barau ya karɓi shugabanni da matasa daga NNPP zuwa APC, inda suka bukaci gyaran madatsar ruwa, kasuwa da kammala ofishin ‘yan sanda a Getso.
Kwamitin da ya tattara rahoto kan zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ya ce an kashe mutane 10, an lalata dukiyar sama da N11bn an jikkata mutane 7.
Aliko Dangote ya samu sabon matsayin cikin jerin masu kudin duniya, Ya dawo na 86 daga na 144 a duniya. Dangote ya shiga cikin masu kudin duniya 100.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fara bibiyar kungiyoyi masu zaman kansu dake jihar domin tabbatar da inda suke samun kudin gudanarwa bayan zargin da aka yi wa USAID.
Shahararren dan wasan kwaiwayo a Kano, Mustapha Naburaska ya ce zai ci gaba da mutunta Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf duk da ya bar jam'iyya.
Gwamnatin kasar Saudiyya ta aikowa Najeirya da tallafin dabino tan 100, za a raba shi a babban birnin tarayya Abuja da Kano a watan azumin Ramadan.
Masu ruwa da tsaki a kasuwar kayan abinci ta Singer sun bayyana yadda saukar farashin Dala, manufofin Tinubu da kaka suka taimaka wajen saukar farashin abinci.
Jihar Kano
Samu kari