Lauyan EFCC Ya Kawo Tangarɗa a Zaman Shari'ar Fitacciyar Ƴar TikTok, Murja Kunya a Kano
- Babbar kotun tarayya da ke zama a Kano ta ɗage zaman yanke hukunci a shari'ar da EFCC ke tuhumar Murja Kunya da laifin liƙi da taka kudi
- Murja Kunya, wacce ta shahara a kafafen sada zumunta musamnan TikTok na fuskantar shari'a ne kan liƙin N400,000 da kuma rawa a kansu
- Mai shari'a Simon Amobeda ya sanya ranar yanke hukunci bayan lauyan EFCC ya buƙaci gyara tuhumar da ake yi wa Murja a zaman jiya Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta sake zama kan shari'ar fitacciyar ƴar TikTok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya.
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'adi watau EFCC ce ta gurfanar da Murja Kunya a gaban ƙuliya kan tuhuma ɗaya tal ta cin mutuncin Naira.

Asali: Facebook
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, EFCC ta tuhumi Murja kunya da yin liƙi da dubban kuɗin Najeriya tare tattaka su a wurin wani shagali a Otal.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A zaman jiya Talata, Mai Shari’a Simon Amobeda, ya dage zaman yanke hukunci da aka tsara kan ƴar TikTok, Murja Kunya, zuwa ranar 20 ga watan Mayu, 2025.
Hakan ta faru ne bayan Lauyan Hukumar EFCC, Musa Isa, ya nemi gyara tuhumar da ake wa Murja, duk da cewa kotun ta rigaya ta tsara yin hukunci a zaman ranar Talata.
Wace tuhuma ake yi wa Murja Kunya?
Murja Kunya, wadda ta shahara a kafafen sada zumunta musamman TikTok, na fuskantar tuhuma daya da ta shafi cin zarafin kudin kasa wato Naira.
EFCC na tuhumarta da watsa Naira har N400,000 da rawa a kai a wani biki da aka yi a Tahir Guest Palace Hotel a watan Disamba na shekarar 2024.
Tuni dai Murja ta amsa laifin a gaban kotu, lamarin da ya ba da damar tsara yanke hukunci domin kawo karshen shari'ar, kamar yadda The Nation ta rahoto.
Lauyan EFCC ya gabatar da sabuwar buƙata
Sai dai bukatar da lauyan EFCC ya gabatar na gyaran tuhumar ne ya kawo cikas a shirin yanke hukunci, kuma ya haifar da sabani tsakanin bangarorin biyu.
Lauyan Murja, Abubakar Saka, ya yi fatali da bukatar, yana mai cewa hakan zai janyo tsaiko ga shari’ar kuma wacce yake karewa na bukatar karin lokaci domin fahimtar sababbin bayanan da aka kawo.

Asali: Instagram
Alkali ɗage zaman yanke hukunci
A karshe, Mai Shari’a Amobeda ya amince da bukatar gyaran tuhumar daga EFCC, sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga Mayu domin ci gaba daga inda aka tsaya.
A halin yanzu, Murja tana ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin kulawar lauya a matsayin sharadin belinta, domin tabbatar da cewa ta halarci kotu a zama na gaba.
Kotu ta ɗaure ƴan TikTok 2 a gidan yari
A baya, kun ji cewa wata kotu a jihar Kano ta yankewa wasu 'yan TikTok hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekara guda kowannensu.
Kotun ta yanke hukuncin cewa ta samu 'yan TikTok din biyu da laifin yada bidiyon batsa, wanda ya saba da da'awar gyaran tarbiya ta jihar Kano.
Wadanda kotun ta yankewa hukuncin su ne, Ahmad Isa da Maryam Musa dukansu ’yan unguwar Ladanai da ke yankin Hotoro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng