Lauyoyin Najeriya Sun Gargadi Abba Kabir kan Saka Dokar Hana Maganar Siyasa a Kano
- Kungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA) ta ce gwamnonin jihohi ba su da hurumin doka wajen tsawatar wa kan da abin da ke cikin shirye-shiryen rediyo da talabijin
- A cewar NBA, matakin da gwamnatin Kano ta ɗauka na hana shirye-shiryen siyasa kai tsaye da sanya wasu ka'idoji da dokoki ya saba wa tsarin mulki
- Kungiyar ta ce hukumar NBC ce kaɗai ke da hurumi na doka da iko bisa tsarin mulkin ƙasa don kula da abubuwan da ake watsa wa a kafafen yada labarai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Kungiyar lauyoyi ta NBA ta yi watsi da matakin gwamnatin Kano na kafa dokokin da za su sarrafa abin da kafafen yada labarai ke yadawa, musamman a rediyo da talabijin.
Gwamnatin Kano ta sanya wasu dokoki da suka shafi hana saka shirye shiryen siyasa kai tsaye a jihar baki daya.

Asali: Facebook
Wani rahoto da jaridar the Cable ta wallafa ya nuna cewa kungiyar NBA ta ce gwamnatin Abba ba ta da hurumin sanya dokar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa dokokin da aka kafa sun samo asali ne daga wani taro da ta yi da masu ruwa da tsaki na kafafen yada labarai a jihar don kiyaye al’adu da mutunta addini.
Amma a wata sanarwa daga shugaban NBA, Afam Osigwe, kungiyar ta ce dokokin sun saba wa sashe na 39 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Kungiyar ta ce kundin mulkin Najeriya ya bayar da 'yancin fadin albarkacin baki da samun bayanai ga kowa da kowa.
Kungiyar NBA ta ce Abba ya wuce gona da iri
A cewar NBA, dokar da Kano ta gindaya da ke haramta shirye-shiryen siyasa kai tsaye da tilasta wa masu shirin rattaba hannu kan yarjejeniyar guje wa kalaman batanci, ya sabawa doka.
The Guardian ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
“Wannan mataki na gwamnatin jihar Kano ya nuna tauye hakkin walwala da ‘yancin bayyana ra’ayi da samun bayanai da doka ta tanada wa kowane ɗan ƙasa.”
Kungiyar ta ce hukumar NBC ce kaɗai ke da ikon doka wajen kula da irin shirye-shiryen da ake watsa wa a kafafen yada labarai bisa ka’idojin ƙasa da kuma tanade-tanaden tsarin mulki.
NBA ta nemi Abba ya janye dokar da ya saka
Shugaban NBA ya ce yunƙurin gwamnatin Kano na dakile shirye-shiryen siyasa, musamman a lokacin da ake buƙatar bude tattaunawa a dimokuradiyya bai dace ba.
Kungiyar NBA ta kara da cewa dokar hanya ce ta durƙusar da ƙwarin gwiwar jama'a da ƙwazon kafafen watsa labarai.

Asali: Facebook
NBA ta bukaci gwamnatin Kano da ta janye matakin nan take, sannan ta nemi hukumar NBC da ta sake tabbatar da ikon ta na doka domin kare ‘yancin fadar albarkacin baki da musayar ra’ayi.
Abba Kabir zai ba malaman Kano rance
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf za ta ba malaman makaranta rancen kudi.
Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa Abba Kabir Yusuf ya ware makudan kudi domin ba malaman makaranta rancen.
Hakan na cikin shirye shiryen gwamnatin jihar na kula da walwalar malaman makaranta da inganta ilimi a fadin Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng