Sheikh Ya Faɗi Matsayarsa da Alkali Abubakar Zaria Ya Ziyarci Shirin Gabon 'Talkshow'
- Wasu malamai sun fara martani dangane da Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria saboda suka kan halartar shirin Gabon 'Talkshow'
- Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya ce ba laifi ba ne halartar shirin, sai dai mutane na neman irin haka daga malamai ba tare da hujja ba
- Malamin ya kara da cewa ya fi dacewa malami ya kame kansa, amma hakan kadai ba laifi ba ne, ya ce mutane suna yawan zagin malamai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wasu malamai sun fara magana kan ce-ce-ku-ce da ake yi kan Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria.
Daga cikin malaman da suka tofa albarkacin bakinsu akwai Sheikh Barista Ishaq Adam Ishaq.

Asali: Facebook
Malami ya tabo batun shirin Gabon 'Talkshow'
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a daren yau Asabar a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Adam Ishaq ya ce abin takaici ne yadda al'umma ke neman laifin malamai domin sukarsu ba tare da hujja ba.
Malamin ya ce abin da Alkali Salihu Zaria ya yi ba laifi be ne sai dai wasu na ganin a matsayinsa na mai wa'azi bai kamata ba.
Shehin ya kara da cewa kamar shi idan aka gayyace shi shirin ba zai je ba amma kuma ba haram ba ne.
Ya ce:
"Wato yana daga cikin hadarin da wannan al'ummar ta shiga mutane har so suke wai a ce malamai sun yi laifi.
"Ba ma wannan ba, malami yana yin wani abu, ba za a duba addini ba, babu ba da uzuri kawai sai zagi.
"Alkali Abubakar Salihu Zaria ya je shirin Gabon 'Talkshow' amma yadda mutane suka dauki abin suna aibata shi wallahi ba daidai ba ne.

Asali: Facebook
Malami ya koka da dabi'un al'umma
Malamin ya ce al'umma yanzu ta fi karkata wurin ganin laifin malamai fiye da abubuwan alheri da suke yi.
Ya kara da cewa:
"Idan kana son kushe shi sai ka ce a matsayinsa na mai da'awa akwai abin da gama-gari za su iya amma kai ba za ka iya yi ba.
"To Alkali Salihu Zaria ya je wannan wuri a matsayinsa na mai da'awa, amma ni aka gayyacen ba zan je ba.
"Ba zan kuma ce wanda ya je ya yi laifi ba, sai dai a matsayinsa na mai da'awa ya kamata yana kamewa amma ba don laifi ba."
Malamin ya ce wurinsa dama a ce ta yi shiga mai kyau na Musulunci to da sauƙi, ya bayyana cewa hakan ya faru ne kawai saboda ya fito a malamai shiyasa.
Gabon: An yi maganganu kan Alkali Zaria
Mun ba ku labarin cewa an samu mabambantan ra'ayoyi bayan amsa gayyatar Sheikh Alƙali Abubakar Salihu Zariya a shirin Hadiza Gabon.
Lamarin ya haifar da muhawara a kafafen sada zumunta inda wasu suka soki halartarsa, suna cewa bai dace malami ya shiga irin wannan dandali ba.
An samu wasu kuma sun kare shi, suna cewa irin wannan dandali yana ba mutane dama su fahimci wasu ɓangarorin rayuwar mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng