Kamar Sarki Sanusi II, Aminu Ado Ya Fara Neman Masu Zuba Jari a Kano

Kamar Sarki Sanusi II, Aminu Ado Ya Fara Neman Masu Zuba Jari a Kano

  • Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya kai ziyara sashin gyare-gyaren jirage na kamfanin Overland Airways domin duba yadda suke aiki
  • An tarbi Basaraken cikin girmamawa daga shugaban kamfanin, Kyaftin Edward Boyo, inda suka tattauna hanyoyin habaka ayyukan jiragen sama zuwa Kano
  • Sarkin na 15 ya nuna goyon baya ga shirin kamfanin na bude sababbin ayyuka a jihar Kano, yana mai fatan hakan zai kawo ci gaba ga yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya fara neman hanyoyin inganta kasuwanci a jihar Kano.

Aminu Ado Bayero ya bukaci wani kamfanin jiragen sama 'Overland Airways' ya fara aiki a jihar Kano domin inganta kasuwanci.

Aminu Ado ya nemo hanyar inganta Kano
Bayan Sanusi II, Aminu Ado ya fara neman masu zuba hannun jari. Hoto: Sanusi II Dynasty, Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Masarautar Kano ya wallafa a manhajar Facebook a yau Laraba 14 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ziyarce-ziyarcen Aminu Ado a Lagos da Kwara

Wannan na daga cikin ziyarce-ziyarcen da basaraken ke yi a kwanakin nan tun bayan halartar wani gagarumin taro a birnin Lagos.

Sarkin Kano na 15 ya samu halartar taron cikar shekaru 50 na aikin jarida da Prince Bisi Olatilo ya shirya.

Rahotan Legit Hausa ya ce taron ya gudana ne a birnin Ikeja na jihar Lagos a safiyar ranar Talata, 13 ga Mayu, 2025, inda manyan baki suka hallara.

Daga bisani an ce basaraken ya wuce birnin Ilorin da ke jihar Kwara domin ganawa da Sarki Dr. Ibrahim Sulu Gambari kan wasu batutuwa masu muhimmanci.

Aminu Ado ya ziyarci kamfanin jiragen sama
Aminu Ado Bayero ya himmatu domin inganta Kano. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: UGC

Aminu Ado ya ziyarci kamfanin jiragen sama

Sanarwar ta ce basaraken ya kai ziyara sashin kula da gyare-gyaren jirage na Overland Airways domin neman hanyar kawo ci gaba a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.

A lokacin ziyarar, an karɓi Sarkin hannu bibbiyu daga mamallakin kamfanin, Kyaftin Edward Boyo, inda suka tattauna batutuwan ci gaban zirga-zirga.

An bayyana cewa Sarkin ya bukaci kamfanin ya fara gudanar da ayyukansa a jihar Kano.

Basaraken ya yi fatan hakan zai kawo sauki a bangaren sufuri da kuma ci gaba ga al'umma.

A cewar sanarwar:

"Mai Martaba Sarkin Kano, Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP yayin tattaunawa tare da ziyarar gani da ido a sashin gudanarwa da gyare gyare (Maintenance & Hangers) na kamfanin jiragen sama na Overland Airways.
"Yayin da Sarki ya samu tarba daga mamallakin kamfanin Kyaftin Edward Boyo, an tattauna yadda kamfanin zai fara zuwa jihar Kano don gudanar da ayyukansa."
"Ran sarki ya dade."

Sarki Sanusi II ya ziyarci kasar Tunisia

A baya, mun ba ku labarin cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya ziyarci kasar Tunisia domin halartar babban taron zuba jari da ciniki na Afrika (FITA2025).

Taron ya gudana ne daga ranakun 6 zuwa 7 ga watan Mayun 2025, a babban otal din Radisson Blu da ke birnin Tunis saboda harkokin ci gaba da zuba hannun jari.

Sarkin ya samu rakiyar manyan masu sarauta daga Kano, ciki har da Sarkin Shanun Kano, Nazir Halliru da Jarman Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.