Bayan Rasa Jiga Jigan NNPP zuwa APC, Kwankwaso Ya Sake Cin Karo da Matsala a Jam'iyya
- Shugaban jam'iyyar NNPP na ƙasa, Dr. Agbo Gilbert Major, ya bayyana cewa Rabi’u Kwankwaso ba ɗan jam’iyyar NNPP ba ne tun 2023
- Gilbert ya ce Kwankwaso da 'yan Kwankwasiyya sun bar jam’iyyar bayan samun sabani, amma mutanen sun nuna ba su da matsala da NNPP
- Ya ce waɗanda suka fice daga jam’iyyar sun gaji da salon mulkin Kwankwasiyya, amma har yanzu suna da alaƙa da shugabancin NNPP
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar NNPP, Dr. Agbo Gilbert Major ya kuma yin magana kan Sanata Rabiu Kwankwaso.
Major ya ce Rabi’u Musa Kwankwaso ba ɗan jam’iyyar ba ne saboda an dade da korarsa daga cikinta.

Asali: Facebook
NNPP ta fadi matsayin Rabiu Kwankwaso
Yayin da yake magana a shirin Daily Politics na Trust TV, Major ya ce jam’iyyarsu ba ta da alaka da Kwankwaso tun 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Bari in fayyace cewa akwai abubuwan da suka fi muhimmanci fiye da Kwankwaso. Ban zo nan in tattauna shi ba.
"Ya zama ɓangare na tarihin NNPP. A wani lokaci ya shigo, daga bisani ya fice tare da Kwankwasiyya. Don haka, ba na son tattauna shi.
Yayin da yake tsokaci kan sauyin sheƙa da ke faruwa a manyan jam’iyyun adawa, Gilbert ya ce Kwankwaso ya shigo jam'iyyar ne da Kwankwasiyya.
“Idan ka duba waɗanda suka sauya sheƙa, za ka ga su ne masu tasiri a Kwankwasiyya, kuma sun taimaka wa NNPP sosai a Kano.
“Don haka, jam’iyyar ta rasa mutanen kirki, ‘yan siyasar kwararru – waɗanda ke da ƙarfin yanke hukunci a siyasa."
NNPP ta fadi dalilin rasa jiga-jiganta
Jigon NNPP ta ta'allaka rashin jiga-jigan jam'iyyar da aka yi musamman a Kano da matsalolin Kwankwasiyya.
Ya kara da cewa:
“Waɗanda suka sauya sheƙa sun gaji da yadda Kwankwasiyya ke tafiya, amma ba su da matsala da NNPP baki ɗaya.
“Rasa Sanata musamman Kawu da wasu mambobin majalisa biyu ba yana nufin tawaye ba ne ga NNPP.
“Mutane sun gaji da tafiyar Kwankwasiyya. Sun ce, ‘mun gaji da salon mulkin mutum ɗaya, mun gaji, za mu bar tafiyar."

Asali: UGC
Major ya magantu kan alakar Kwankwaso da Gwamnati
Major ya ce kyawun dimokuraɗiyya shi ne sassauci ga ‘yan siyasa don su sauya jam’iyya idan ba su jin daɗi a inda suke.
Da aka tambaye shi ko yana damuwa da kusancin Rabiu Kwankwaso da fadar gwamnati, Gilbert ya ce:
"Shin za ka damu da wanda ya daina zama ɗan jam’iyyar ka fiye da shekara ɗaya, yana shiga wata tafiya?
“Me zai sa hakan ya dame ni? Don Allah, mu tattauna muhimman abubuwa, mutumin ya tafi."
'Yan majalisun NNPP sun koma jam'iyyar APC
Kun ji cewa ‘Yan majalisar wakilai biyu daga Kano sun fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Yan majalisar sun hada da Abdullahi Sani Rogo da Kabiru Usman Alhasan Rurum, wadanda ke wakiltar mazabun Rano/Bunkure/Kibiya da Karaye/Rogo.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu fitattun ‘yan NNPP ciki har da Sanata Kawu Sumaila suka koma APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng