Bayan Dawowar Sanusi II daga Tunisia, Aminu Ado Bayero Ya Dura a Lagos

Bayan Dawowar Sanusi II daga Tunisia, Aminu Ado Bayero Ya Dura a Lagos

  • Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya samu halartar taron cikar shekaru 50 na aikin jarida da Prince Bisi Olatilo ya shirya
  • Taron ya gudana ne a birnin Ikeja na jihar Lagos a safiyar Talata, 13 ga Mayu, 2025, inda manyan baki suka hallara
  • Hakan na zuwa ne bayan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya dawo daga kasar Tunisia bayan halartar taron tattalin arziki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Sarkin Kano na 15, ya bar jihar Kano domin halartar taro na musamman a jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya.

Basaraken ya tafi jihar ne yayin da ake dakon hukuncin kotun koli game da sarautar jihar Kano da ake yi wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Aminu Ado ya ziyarci Lagos domin babban taro
Aminu Ado ya dura a Lagos domin gagarumin taro. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Shafin Masarautar Kano ne ya tabbatar da haka a yau Talata 13 ga watan Mayun 2025 a manhajar Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi II ya dawo daga taro a Tunisia

Ziyarar Mai Martaba Aminu Ado Bayero na zuwa ne bayan Sarki Sanusi II ya dawo daga kasar Tunisia.

Sanusi II ya je kasar Afrikar ne domin tattauna batutuwan tattalin arziki da neman masu zuba jari a Kano.

Ziyarar basaraken ya jawo maganganu a kafafen sadarwa inda wasu ke bayyana amfanin Sarkin a bangaren tattalin arziki.

Har ila yau, wasu na cewa hakan ya ragewa Gwamna Abba Kabir Yusuf aiki wurin zakulo masu zuba jari a jihar.

Dukkan wadannan ziyarce-ziyarcen na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin kotun koli game da rigimar masarauta a jihar.

Sanusi II da Aminu Ado na ci gaba da jiran hukuncin karshe kan kujerar Sarkin Kano da ke daya daga cikin karaga mafi muhimmanci a Arewacin Najeriya.

Aminu Ado ya je Lagos bayan dawowar Sanusi II
Bayan dawowar Sanusi II, Aminu Ado Bayero ya shiga Lagos. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Asali: Twitter

Aminu Ado ya halarci babban taro a Lagos

A bangarensa, Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero, ya halarci wani babban taron ne domin murnar cikar shekaru 50 na aikin jarida.

Taron na musamman an shirya shi ne domin tunawa da gudummawar da Prince Bisi Olatilo ya bayar a fannin aikin jarida tun farkon aikinsa.

Majiyoyi sun ce ana gudanar da taron ne a yau Talata, 13 ga watan Mayun shekarar 2025 a Lagos da ke Kudancin Najeriya.

Sanarwar ta ce:

"Daga birnin Ikkon jihar Lagos inda Mai Martaba Sarkin Kano, Alh Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya halarci taron cikar shekaru 50 cikin ayyukan jarida (journalism) na PRINCE BISI OLATILO a safiyar yau Talata 13 ga watan Mayun 2025, ran Sarki ya dade."

Motocin masarauta: Gwamna Abba ya kare kansa

Kun ji cewa Gwamnatin Kano ta kare kanta kan kudi N670m da aka ware don gyara da sayen motocin Sarki Muhammadu Sanusi II, ta ce hakan daidai ne.

Kwamishinan yada labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce gwamnatin jiha na da alhakin kula da sarakuna, ciki har da sayan masu motoci.

Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin Mallam Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje ma an sayawa sarakuna sababbin motoci ba tare da cece-kuce ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.